Safiyanu Dantala Jobawa
An bukaci al’ummar karamar hukumar Garun mallam da su ba da gudunmawar da ta dace wajen sanar da bullar wata cuta don dakile ta cikin sauri.
Hakan na zuwa ne daidai lokacin da ma’aikatar lafiya ta karamar hukumar Garun mallam ke gudanar da bada horo na musamman ta hanyar zabo wakilai daga kowacce unguwa daban-daban don gudanar da aikin wanda kungiyar (THE GLOBALFUND)ta duniya ta dauki nauyin shirin, hadin gwiwa tare da gwamnatin tarayya da jiha da kuma ta karamar hukuma don yaki da cututtuka masu yaduwa a cikin al’umma.
Kano a Shirye Take ta Yaki Kwalara da Sauran Cututtuka – KNCDC
Da ya ke karin haske a wajen bada horon, Malam Ibrahim Yusif Isma’il Madobi, ya ce “An tsara hakan ne da nufin samun sauki wajen sanar da bullar wata cuta da ta shafi bil’adama da kuma dabbobi kamar su;- ( Kyanda,Mashako,Tarin fuka TB, da zazzabin maleriyaAmai da gudawa d.s) masu saurin yaduwa a cikin al’umma don kawo daukin gaggawa tare da magance ta cikin sauri ba tare da wani jinkiri ba.
Isma’il Madobi, ya ce “ Mahalarta taron sun hadar da Masu unguwani da masu maganin gargajiya da unguwar-zoma da wanzamai da kuma kungiyar cigaban gari da dai sauransu, a matsayin wakilan hukamar lafiya wanda ake kira da (Community Base Surveillance).
Kwamishinan Lafiya Ya Yabawa K/H Uku Akan Rigakafin Shan Inna
Aikin su shi ne, sa idanu da neman ainihin sahihin bayyanin bullar cuta tare da sanar da hukumar lafiya.
A karshe jagoran shirin bada horan, Malam Ibrahim Yusif Isma’il Madobi (LGA-WHO) ya bukaci Mahalarta horon da su yi aiki da irin horon da aka ba su tukuru tare da bada cikyankyan hadin-kai da goyan bayan ganin an samu al’umma masu cikyakkiyar lafiya.
An gudanar da shirin bada horon ne, na kwanaki biyu a cibiyar musulunci da ke karamar hukumar Garun mallam, wanda ya samu wakilcin daya daga hukumar cibiyar bincike ta kasa wato (NCDC), Mr Ibrahim Kaa.
Gwamnatin Jihar Kano Ta yi Kira Ga Alumma Akan Cutar Kwalara
Inda ya gode wa mahalarta horon bisa hadin kan da suka bayar don ganin shirin ya samu nasara a yankunansu.
A nasa jawabin shugaban majalisar karamar hukumar Hon Barr Aminu Salisu Kadawa ya gode wa wannan hukumar ta Globalfund da ma’aikatar lafiya da mahalarta horon bisa wannan shirin, kuma ya ce “A shirye su ke wajen bada gudunmawar d ta ce domin samun wannan shirin.