Amurka na shirin hana ƴan Nijeriya zuwa haihuwa a ƙasar
Ofishin Jakadancin Amurka da ke Najeriya ya fitar da gargaɗi cewa duk wani mai neman biza da aka gano cewa tafiyarsa zuwa ƙasar ta haihuwa ce da nufin samawa jaririn da za a haifa takardar shaidar zama ɗan ƙasa to za a hana shi shiga ƙasar.
Wannan gargaɗi ya fito ne ta shafin na X @USinNigeria a yau Litinin.
Ofishin jakadancin ya jaddada cewa jami’an bayar da biza za su ƙi amincewa da buƙatun biza idan sun fahimci cewa babban dalilin tafiyar mutum shi ne haihuwa a Amurka.
Daily Nigerian Hausa