Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhinin rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Alhaji Muhammadu Buhari.
Ya bayyana Buhari a matsayin babban mutum wanda rayuwarsa ta kunshi ƙaunar ƙasa, ɗabi’a ta gaskiya, da rikon amana.
A cikin wata sanarwa ta ta’aziyya, Gwamna Yusuf ya bayyana Buhari a matsayin jagora wanda ya ƙaddamar da rayuwarsa ga hidimar Najeriya, tun lokacin da yake mulki a matsayin soja har zuwa lokacin da aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa ta hanyar dimokuraɗiyya.
Buhari’s Leadership Will Inspire Future Generations-NAWOJ
“Shugaba Muhammadu Buhari ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen hidima ga ƙasarmu mai albarka cikin gaskiya da jarumtaka,” in ji Gwamna Yusuf.
“Tsayuwarsa akan gaskiya, sauƙin hali da kuma jajircewarsa wajen inganta rayuwar talakawa za su ci gaba da zama abin koyi ga al’umma.”
Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, gwamnatin da al’ummar Jihar Katsina, da kuma daukacin ‘yan Najeriya bisa wannan babban rashi.
Tinubu Confirms Buhari’s Death, VP Shettima to Escort Body From Uk
Ya kuma yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa, ya sa masa albarka, ya shigar da shi cikin Aljannatul Firdaus, tare da bai wa al’umma haƙurin jure wannan babban rashi.