Gwamnatin Jihar Imo ta haramta gudanar da bikin yaye ga ɗaliban Nursery da JSS3, domin rage nauyin kuɗi ga iyaye tare da mai da hankali kan harkar karatu.
Kwamishinan Ilimi, Farfesa Bernard Ikegwuoha, ne ya sanar da wannan sabon tsari a wata takardar umarni da ya fitar a ranar 15 ga Agusta, 2025, wacce aka aika wa iyaye, masu kula da yara da kuma masu makarantu.
Umarnin, wanda ya fara aiki nan take, ya amince da bikin yaye ne kawai ga ɗaliban Primary 6 da kuma SSS3, kamar yadda tsarin ilimi na Najeriya 6-3-3-4 ya tanada.
An Cire wa Dalibai Mata 125 Kaya a Makaranta Saboda Jinin Al’ada
“Ma’aikatar ta kuduri aniyar samar da ingantaccen ilimi ga dukkan ɗaliban jihar,” in ji kwamishinan. “An soke bikin yaye ga ɗaliban Kindergarten, Nursery da JSS3.
Wannan tsari zai taimaka wajen mai da hankali kan nasarorin ilimi a ƙarshen matakan firamare da sakandare.”
Ikegwuoha ya kuma tabo matsalar canza littattafai duk shekara a makarantu masu zaman kansu da na addini, yana mai cewa hakan babban nauyi ne ga iyaye.
Ya bayar da umarni cewa littattafan da aka amince da su za a yi amfani da su na tsawon aƙalla shekaru huɗu, domin ɗan’uwa da ke biye a makaranta ya amfana da su.
Azhan Noor Islamiyya Shines Bright in Kano : Celebrates Quranic Graduation
“Mun gargadi masu makarantu da su daina canza littattafai akai-akai,” in ji shi. “Amfani da jerin littattafan da aka amince da su na tsawon shekaru huɗu zai kawo daidaito, ya rage kuɗin da iyaye ke kashewa, kuma ya ƙarfafa yanayin koyo mai ɗorewa.”
A cewar kwamishinan, waɗannan matakan sun haɗa da tsarin inganta ilimi mai inganci da ɗorewa, wanda zai amfani ɗalibai, iyaye, da kuma al’umma gaba ɗaya.
Instablognja