A wani yunƙuri na ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya don inganta tsaro da samar da guraben aiki ga matasa, wani babban kwamiti daga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Harkoki na Musamman, Alhaji Nasiru Sule Garo, ya kai ziyarar aiki ga Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, a ofisoshinsu dake Abuja.
Manufar wannan ziyara ita ce ƙarfafa dangantaka da haɗin kai tsakanin matakan gwamnati don bunƙasa damar shiga aikin soja, Civil Defence, Hukumar Shige da Fice da sauran hukumomin tsaro, musamman ga matasan Jihar Kano.
Gwamnatin Kano zata Sabuntawa Ma’aikatan Shara Kayan Aiki
Alhaji Nasiru Garo ya jaddada kudirin Gwamnatin Kano na yin amfani da haɗin gwiwar da gwamnati ta tarayya domin faɗaɗa damar shiga aikin gwamnati ga ’yan asalin jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa, gwamnati na ƙoƙarin ganin an cike guraben aiki da ake da su a hukumomin tsaro, tare da ƙara yawan kujerun da ake ware wa Jihar Kano bisa ƙa’idojin tsarin raba guraben aiki na ƙasa.
Ya ce, Sakataren Zartarwa na Hukumar Shawarwari da Neman Aiki ta Jiha zai ci gaba da yin aiki tare da hukumomin daukar ma’aikata na sojoji da na paramilitary don cimma wannan manufa.
Wakilan da suka raka kwamishinan sun hada da Alhaji Ado Danjummai Wudil, Sakataren Zartarwa, Hukumar Shawarwari da Neman Aiki; Alhaji Ibrahim Mohammed Kabara, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Musamman; Ibrahim Abdulkarim, Daraktan Harkokin Gabaɗaya da Gudanarwa; da Murtala Iliyasu, Daraktan Shawarwari.
An Shigar Da Korafi Gaban Majalisa Akan Karin Waadin Aiki a Kano
A jawabansu na maraba da tawagar, Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, sun yaba da wannan ziyara tare da bayyana ta a matsayin mataki na hangen nesa kuma mai muhimmanci.
Sun jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi yana da matuƙar amfani wajen bunƙasa tsaro da ci gaban tattalin arziki. Ministocin sun kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa irin kokarinta na tallafa wa matasa, tare da alkawarin ganin an bai wa Kano guraben da suka dace da yawan jama’arta da muhimmancin jihar a ƙasa baki ɗaya.