Ma’aikatar Kimiyya, Fasaha da Ƙirƙira ta Jihar Kano (KSMSTI) ta sanar da haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Makamashi ta Ƙasa (ECN) domin hanzarta samar da tsaftataccen makamashi da kuma ƙarfafa ci gaban da ke karkashin da ƙirƙira a fadin jihar.
Wakilan Ma’aikatar, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Kimiyya, Dr. Yusuf KofarMata, sun samu tarba daga Darakta-Janar na ECN, Dr. Abdullahi Mustapha, a yayin wata babbar ziyarar zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja.
Muhimman batutuwan da aka tattauna a yayin ziyarar sun haɗa da: samar da wutar sola a manyan cibiyoyin gwamnati kamar asibitoci, jami’o’i da cibiyoyin ƙirƙira.
Sauran sun haɗa da gudanar da bincike kan amfani da makamashi da samar da fitilun titi masu amfani da hasken rana, da hanyoyin samun ruwa ba tare da dogaro da wutar lantarki ba.
A cewar wata sanarwa daga KSMSTI, ganawar ta tattauna batun haɓaka manufofin makamashi na Jihar Kano, tsarin makamashi da kuma dogon shirin raya wannan fanni.
Dr. KofarMata ya isar da gaisuwar Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na amfani da sabbin fasahohin makamashi don samar da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Haka kuma, ya gabatar da tayin buɗe ofishin ECN na shiyya a Jihar Kano, wanda Darakta-Janar na ECN ya karɓa hannu bibbiyu, tare da bayyana shirinsa na zurfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin biyu.
Ya sanar da cewa za a kafa kwamiti na fasaha na haɗin gwiwa nan da nan domin aiwatar da waɗanda aka cimma matsaya a kai cikin tsari da sauri.
Daily Nigerian Hausa