Wata Babbar Kotun Jihar Kaduna ta sake ƙin bayar da beli ga tsohon Shugaban Ma’aikata na tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Alhaji Bashir Sa’idu.
El-Rufa’i Sues Kaduna House Of Assembly Over N432 Billion Claim
Kotun ta umarci a sake maida shi gidan gyaran hali bayan gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume 10 da suka shafi zargin almundahana, wawure kuɗi, da sata a Gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai.
ICPC Takes Ex-Kaduna Commissioner to Court Over N155 Million
Yayin gabatar da shari’ar a gaban Mai Shari’a Isa Aliyu a ranar Talata, an karanta tuhume-tuhumen 10 a gaban Alkali, inda ya musanta su baki ɗaya.
Cikin tuhume-tuhumen, an zargi tsohon kwamishinan da sayar da dala miliyan $45 na gwamnatin Jihar Kaduna—daidai da Naira biliyan 18.45.
Kaduna Ultra-Modern Hospital Nears Completion
An kuna yi Zargin cewa a lokacin ya sayar da ko wace dala daya akan farashin Naira 498 a kan kowace dala, wanda hakan ya jawo hasarar Naira biliyan 3.96 ga gwamnatin jihar.
A cewar masu gabatar da ƙara, an ce laifin ya faru ne a shekarar 2022, lokacin da Sa’idu yake matsayin Kwamishinan Kuɗi a gwamnatin El-Rufai.
Masu gabatar da ƙara sun ƙara bayyana cewa, suna zargin Sa’idu ya yi almundahana da Naira biliyan 3.96, wanda ya saɓa wa Sashe na 18 na Dokar Hana Almundahana ta 2022.
Lauyan wanda ake tuhuma, M.I. Abubakar, ya sanar da kotun cewa akwai buƙatar kotun ta bayar da beli ga wanda yake karewa, Alhaji Bashir Sa’idu, domin ya riga ya shafe kwanaki 21 a tsare tun bayan da aka kama shi a ranar 2 ga Janairu, 2025.
Ya kuma bayyana wa kotun cewa an gabatar da buƙatar beli tun ranar 16 ga Janairu, yana mai cewa bayar da beli zai bashi damar yin shirin kare kansa yadda ya kamata kan tuhume-tuhumen da ake masa.
Sai dai Lauyan masu gabatar da ƙara, Farfesa Nasiru Aliyu, ya ƙi amincewa da buƙatar belin, yana mai cewa doka ta tanadi a bawa masu gabatar da ƙara kwanaki bakwai domin gabatar da amsar su kan buƙatar belin.
Bayan hutun mintuna 40, Mai Shari’a Isa Aliyu ya yanke hukunci cewa a ba masu gabatar da ƙara isasshen lokaci kamar yadda doka ta tanada domin su gabatar da nasu amsar kan buƙatar belin.
Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 23 ga watan Janairu, 2025 domin sauraron buƙatar belin.