Wata kotun ɗaukaka ƙara a Amurka ta jaddada hukuncin kama shugaban Amurka mai jiran gado, Doald Trump, da laifin cin zarafi da kuma ɓata sunan ‘yarjarida E. Jean Carroll.
Kotun ta ci tarar Trump dala miliyan biyar game da tuhumar.
Shari’ar ta ji bahasi kan wani hari da ya faru a shekarar 1990 a New York, da kuma yunƙurin da Trump ya yi na yin watsi da batun a matsayin ƙarya.
A wani lamari mai kama da wannan, an umarce shi ya biya Ms Caroll sama da dala miliyan 80 saboda ɓata suna, da kuma kimarta.
Shugaban ya ɗaukaka ƙara a kan wannan ma.
BBC HAUSA