Mambobin Kwamitin Gasar Karatun Alƙur’ani na Jihar Kaduna sun kai wa Gwamna Uba Sani ƙorafi kan zargin almundahana da rashawa da ake yi wa mai tsara harkokin gasar na dindindin, Sheikh Jamilu Abubakar wanda aka fi sani da Albany.
Sun zargi Albany da nuna halin girman kai, rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen gasar da kuma cin zarafin mambobin kwamitin tun lokacin da aka nada shi a shekarar 2015.
Farin Dutse Community Celebrates Abduljabbars’ Quranic Recitation Victory
A wata takardar ƙorafi da aka aika wa gwamnan a ranar 15 ga Yuli, wadda shugaban kwamitin ya sanya wa hannu tare da wasu masu ruwa da tsaki guda 22, sun bayyana yadda Albany ya gaza gabatar da rahoton kuɗi da ayyukan kwamitin tsawon shekaru takwas da suka gabata.
“Tun daga shekarar 2015 babu wani rahoto na ayyuka, taruka da aka gudanar da aka gabatar wa mambobin kwamitin ko hukumomin da suka dace. Ya ƙi bayyana asusun kuɗin shiga da fita duk da matsin lambar da ake yi masa. Sai ma ya riƙa cewa shi kadai ne ke ɗaukar nauyin gasar tun hawansa,” in ji ƙorafin.
Sun kuma ce Albany ya karkatar da kuɗaɗen da aka ware don mahalarta gasar da alkalan gasar, ciki har da kuɗin da Gwamnan jihar ya bayar a 2022. Sun bayyana cewa rashin gaskiyar tasa ya jawo tabarbarewar aikin kwamitin da mutuncinsa a idon jama’a.
Yobe Annual Qur’anic Recitation Commences in Gashua.
“Albany ya gaza sauka daga wannan mukami duk da yana riƙe da manyan kujeru biyu na siyasa a jihar – shugaban ƙaramar hukumar Sabon Gari da kuma shugaban ALGON na jihar Kaduna – lamarin da ke kawo cikas ga gudanar da ayyukan kwamitin,” inji su.
Masu ƙorafin sun ce halayensa na iya bata sunan gwamnatin Gwamna Uba Sani mai mayar da hankali kan harkokin addini da kuma rage yarda da gwamnatin a idon al’umma.
Da aka tuntubi Albany don jin ta bakinsa, bai ɗauki wayar da aka kira shi ba, kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba.
Sai dai kuma wata kungiya ta masu ruwa da tsaki a fannin karatun Alkur’ani sun ƙaryata zage-zagen da ake wa Albany.
A wata takarda da suka aikewa DAILY NIGERIAN a yau Lahadi, sun ce zage-zagen shifcin gizo ne kuma karya ne, inda su ka ce an yi ne don a bata masa suna.
Daily Nigerian Hausa