Ƙungiyar likitocin Jihar Legas (Medical Guild) ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na kwanaki uku daga karfe 8:00 na safe a ranar Litinin, 28 ga Yuli, 2025, sakamakon cire musu albashi da suka ce an yi ba bisa ka’ida ba.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Japhet Olugbogi, ya ce gwamnatin jihar ta fara rage albashi tun watan Afrilu ba tare da tattaunawa ba, duk da kafa kwamitin sasanci, an sake cire wani kaso daga albashin watan Yuli.
Ƙungiyar na neman a mayar da kuɗin da aka cire cikin gaggawa, tare da ba da wa’adin kwanaki 21, inda suka yi gargaɗin shiga yajin aikin dindindin idan ba a biya buƙatunsu ba.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan halin da sashen lafiya ke ciki da kuma matsin rayuwa da ke haddasa barin ƙasa da likitoci ke yi. Ta roƙi Gwamna Babajide Sanwo-Olu da ya shiga tsakani domin dakile tabarbarewar lafiyar al’umma.
Daily Nigerian Hausa