Abdulmajid Habibu Isah

Jam’’iyyar hamayya ta PRP, ta ce Najeriya ba ta samu cigaban azo-a-gani ba cikin shekara 64 da samun ‘Yancin kai da kuma shekara 25 na mulkin Demukuradiyya ba tare da katsewa ba.

APC Charges Governor Lawal to Prioritize Security Over Politics

Wannan na kunshe ne cikin sakon sabuwar shekara dauke da sahannun Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PRP na Arewa maso Yammacin Najeriya, Abba Sule Namatazu, inda Jam’iyyar PRP ke taya ‘Yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2025.

Namatazu ya ce bisa la’akari da shekarun da aka shade, kamata ya yi Najeriya ta fita daga cikin kasashen dake fama da talauci da rashin tsaro da cin hanci da rashawa, Sai dai hakan bata sami ba saboda rashin Ingantaccen Shugabanci a shekara 25 daga 1999 zuwa Yau.

Kazalika Jam’iyyar PRP ta yi Allah wadai da kawo yanzu wasu jihohin ba sa biyan mafi karancin albashi duk da cire tallafin Man fetur da ya jefa rayuwar ‘Yan Nigeria cikin kunci, kuma tana sane da shirin Gwamnatin Tarayya na mayar da wasu makarantu Gwamnati masu zaman kansu da hakan ka iya tilastawa matasa da dama barin Makaranta wasu su fada aikata laifika yayinda rashin tsaro ke kara ta’azzara zuwa sassan Kasa baki daya.

Kano Royal Family Denies Politics Behind Wedding Venue Shift

Daga nan, Matazu ya yi kira ga Gwamnatoci a kowane mataki da su kara kaimi a fannnin Aikin Gona, lafiya, Ilimi, Tsaro da sauraran fannonin cigaban Al’umma, bugu da kari Jam’iyyar PRP ta bukaci ‘Yan Najeriya da su tabbatar da Kyakkyawan Shugabanci da kuma bibiyar shugabanni.

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version