Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke haramcin sanya siket ga ƴan bautar ƙasa mata da NYSC ta yi.
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Hauwa Joseph Yilwa ta bayyana cewa tilasta mata sanya gajeren wando a matsayin tufafin da hukumar ta NYSC ta amince da shi ya saɓawa ‘yancin addini da mutuncin ɗan’adam da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.
Daily Trust ta rawaito cewa wasu tsoffin ƴan bautar kasa guda biyu – Ogunjobi John Blessing da Ayuba Vivian – wadanda aka hana su takardun shaidar kammala shirin hidimar ƙasa saboda ƙin sanya gajeren wando ne su ka shigar da ƙara daban-daban, su na ƙalubalantar matakin NYSC, inda kotun ta haɗe ƙararrakin biyu waje guda.
A hukuncin ta, Mai Shari’a Yilwa ta bayyana cewa ƙin amincewa da sanya siket a matsayin wani ɓangare na tufafin na NYSC ya saɓawa hakkinsu da ke kunshe a Sashe na 38(1) na Kundin Tsarin Mulki na Ƙasa na 1999 (wanda aka yunwa kwaskwarima), da kuma Littafin Bible 22:5.
Kotun ta kuma umurci NYSC da ta biya diyya ta Naira miliyan goma (₦10,000,000).
Daily Nigerian Hausa