Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta bayyana cikakken goyon baya ga kokarin al’umma na rage aikata laifuka da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Shugaban Majalisar, Malam Ibrahim Khalil, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar ƙungiyar farar hula ta “San Makwabciyar ka” a ofishinsa da ke Kano.
Council of Jumu’at Imams Supports Move to Regulate NGOs
Malam Khalil ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin shugabannin addini, ƙungiyoyin farar hula da hukumomin gwamnati wajen yaki da matsalolin tsaro.
NILDS Hosts Prof. Gani’s Presentation on Almajiri School System
Ya yaba da yadda ƙungiyar ke aiki daga tushe don tallafa wa gwamnati wajen tabbatar da tsaro, tare da tabbatar da goyon bayan Majalisar ga duk wani shiri da ke da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Tun da fari, shugaban ƙungiyar “San Makwabciyar ka”, Kwamared Muhammad Sani Garba, ya bayyana cewa sun kai ziyara ga Majalisar ne domin neman haɗin gwiwa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin sanya ido a unguwanni da kuma gargadin su kan haɗurran da ke tattare da ayyukan laifi kamar damfarar waya, shan miyagun kwayoyi da sauran abubuwan da ke barazana ga zaman lafiya.
Ya bayyana cewa ƙungiyar na da niyyar tallafa wa ƙoƙarin gwamnati ta hanyar karfafa wayar da kan jama’a da kuma gina dangantaka mai kyau tsakanin mazauna unguwanni domin gano da kuma kai rahoton duk wani abu da ke iya janyo hatsari.
Shirin “San Makwabciyar ka” wata ƙungiyar farar hula ce da ke da nufin tabbatar da tsaro ta hanyar gina amincewa da haɗin kai tsakanin mazauna unguwanni don hana aikata laifuka da kuma ɗaukar mataki cikin gaggawa kan barazanar tsaro.