A jihar Kano, an kammala babban musabaƙar karatun Alƙur’ani mai tsarki da Sanata Bashir Garba Lado ya shirya, inda aka raba kyaututtuka masu yawa ga zakarun gasar.
Ahmad Shuaibu, wanda ya wakilci ƙaramar hukumar Shanono, ya lashe gasar a rukuni na izifi 60 kuma ya samu gida, kujerar Umrah, kuɗi har Naira miliyan ɗaya, da tallafin karatu daga gwamnatin Qatar har zuwa jami’a.
Kano Gov Awards Hajj Seats To Winners of Qur’anic Competition
Haka kuma, Maryam Abubakar Muazu daga ƙaramar hukumar Dala, ta yi nasara a wannan rukuni, inda ita ma ta samu irin waɗannan kyaututtuka.
Sauran wanda suka zo na biyu da na uku a dukkan rukunan gasar suma sun samu kyaututtuka iri-iri da suka haɗa da babura masu kafa uku da biyu, kuɗi, shaddoji, atamfofi da tallafin karatu.
KHAIRUN Celebrates International Qur’anic Recitation Champion
A jawabinsa yayin rabon kyaututtukan, Sanata Lado — wanda aka fi sani da Ladon Alheri — ya ja hankalin iyayen yara da su tabbatar an yi amfani da kyaututtukan yadda ya dace.
Ya ce ya shirya musabaƙar ne domin tunawa da irin ayyukan alheri da mahaifiyar shugaban kasa, Hajiya Abibat Mogaji Tinubu, ta yi kafin rasuwarta.
Sanatan ya bayyana cewa musabaƙar ta gudana ne domin nuna muhimmancin karatun Alƙur’ani da lada da ake samu daga hakan.
Haka kuma ya ce an bayar da damar zuwa Umrah domin zakarun su kara samun tsoron Allah da kyawun zuciya. Musabaƙar ta ɗauki tsawon wata ɗaya kafin a kammala ta.