Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe kudi sama da naira biliyan 36 a ayyuka daban daban musamman wadan da za su shafi Al’ummah kai tsaye.
Hakan na zuwa ne a zaman da majalisar zartarwar jihar ta gudanar a Jiya Litinin.
Da yake karin haske kan zaman kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce, gwamnatin ta kaddamar da wani kwamati na musamman da zai yi duba kan yadda za a samar da gyara a gidajen yarin dana kula da kanana Yara wato Remand home.
Waiya ya kuma ce duba da karatowar damuna majalisar ta amince a fitar da kudade dan gudanar da aikin kwalbatoci a fadin jihar.
Da yake jawabi kwamishina ayyuka Injiniya Marwan Ahmad, ya ce gwamnati za ta kwace duk wani aiki na 5 kilomita da aka baiwa dan kwangilar da ya tsaya yana jan kafa a kansa.
Kwamishina Ya Mayar Wa Gwamnatin Kano Rarar Naira Miliyan Dari
Shi kuwa kwamishinan gidaje na Kanon da shima ya kasan ce a gurin Akitak Ibrahim Yakubu Adamu cewa ya yi, gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar da za ta gyara matsalolin ruwan da ake fuskanta a jihar.