Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe kudi sama da naira biliyan 36 a ayyuka daban daban musamman wadan da za su shafi Al’ummah kai tsaye.
Waiya ya kuma ce duba da karatowar damuna majalisar ta amince a fitar da kudade dan gudanar da aikin kwalbatoci a fadin jihar.
Read also: Kano Pillars Volleyball Hails Gov Yusuf for Sports Support
Da yake jawabi kwamishina ayyuka Injiniya Marwan Ahmad, ya ce gwamnati za ta kwace duk wani aiki na 5 kilomita da aka baiwa dan kwangilar da ya tsaya yana jan kafa a kansa.
Read also: NDC Candidate’s Omission: Kwankwasiyya Protests in Kano
Kwamishina Ya Mayar Wa Gwamnatin Kano Rarar Naira Miliyan Dari
Read also: Kano SUBEB Approves Soft Loans, Whiteboards for Teachers
Shi kuwa kwamishinan gidaje na Kanon da shima ya kasan ce a gurin Akitak Ibrahim Yakubu Adamu cewa ya yi, gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar da za ta gyara matsalolin ruwan da ake fuskanta a jihar.
Ya kuma ce majalisar ta sanya hannu wajen inganta gidan adana namun daji da hukumar yawon buda idanu da dai sauran su.

