Biyo bayan ruwan sama mai yawa da ya haddasa ambaliya a unguwannin Kurna da Kewayen Zagaye na Baban Gwari, Gwamnatin Jihar Kano ta fara daukar matakan gaggawa domin gano musabbabin lamarin da kuma dakile faruwar hakan nan gaba.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dr. Dahir Hashim, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar gani da ido tare da Kwamishinan Ayyuka da Ababen More Rayuwa, Injiniya Marwan Ahmad, domin tantance halin da ake ciki.
Lagdo Dam at Low Level, No Flood Risk from Cameroon-FG
Duk da ci gaba da aikin share magudanan ruwa da gwamnatin ke yi, Dr. Hashim ya bayyana abin da suka gani a ziyarar a matsayin abin tada hankali.
Ya ce, ’yan kasuwa daga kasuwar Kofar Ruwa har zuwa Baban Gwari suna zubar da shara cikin magudanan ruwa ba tare da kula ba, sannan kuma gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba sun rufe hanyoyin ruwa.
“’Yan kasuwa na zubar da shara cikin magudanan ruwa babu tsari, sannan an gina gidaje da shaguna a kan hanyoyin ruwa. Wannan shi ke haddasa cunkoso da ambaliya — kuma ba za mu lamunta da hakan ba,”
A cewarsa, an fara aikin tono da share magudanan ruwa a unguwar Kurna, yayin da Hukumar Tsara Birane ta Kano (KNUPDA) ta riga ta yi wa gine-ginen da ba bisa ka’ida ba alamar rushewa a Baban Gwari, domin bude hanyoyin ruwa yadda ya kamata.
Flooding:Jigawa Enviromental Agency Desilts Nine High Risk LGAs
Dr. Hashim ya kara da cewa suna kammala tattara cikakken rahoto kan abubuwan da suka gano da kuma matakan da aka fara dauka, wanda za a mikawa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin yanke shawara, ciki har da yiwuwar fadada magudanan ruwa a yankunan da abin ya shafa.
Ya kuma yi gargaɗi ga al’umma da ’yan kasuwa:
“Wannan gwamnati ba za ta lamunci zubar da shara barkatai ko kuma gina gine-ginen da ke kawo barazana ga rayuka da dukiyoyi ba. Ina kira ga al’umma da su daina irin wadannan halaye.
Gwamnati za ta dauki matakin da ya dace domin kare rayuka da muhalli.”