Gwamnatin jihar Kano KNSG ta ce zata daga darajar asibitin Masarautar Karaye izuwa asibitin kwararru domin inganta harkokin lafiya.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin karbar bakuncin Kwamitin lafiya na Masarautar Karaye karkashin jagorancin Matawallen Farfesa Kamilu Musa a ofishin sa.
KNSG Signs N12.7bn Kankara-Karaye Road Project
Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada kudirin Gwamnatin Kano a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na daga darajar asibitin Masarautar Karaye zuwa asibitin kwararru, tare da samar da kayan aiki na zamani domin inganta kula da lafiyar al’ummar yankin.
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnati ta kuduri aniyar inganta kiwon lafiya a fadin jihar, musamman a yankunan karkara, domin tabbatar da adalci da saukin samun kula da lafiya ga kowa da kowa.
A yayin ziyarar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya kafa wani kwamitin musamman da zai binciki bukatun yankunan Karaye da Rogo, domin tsara yadda za a samar da kayayyakin aiki na zamani da kuma karin ma’aikatan lafiya.
Gov Yusuf’s N3B Education Reform Earns K-SAFE Commendation
Kwamitin zai kasance a ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya Pharmacist Aminu Bashir.
Da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Lafiya na Masarautar Karaye, Farfesa Kamilu Musa Karaye wanda shi ne Matawallen Karaye, ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce neman haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya wajen inganta asibitocin yankin, da kuma samar da kayayyakin aiki da suka dace da zamani, la’akari da yawan jama’ar da masarautar ke kula da su.
Farfesa Karaye ya kuma yi fatan ganin an tura karin ma’aikatan lafiya zuwa cibiyoyin lafiya na yankin, tare da nuna cewa daga matsayin asibitin zai taimaka matuka wajen rage cinkoson marasa lafiya a manyan asibitoci na cikin birni.
Ya yaba da irin kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen inganta harkokin lafiya a fadin jihar.