Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana shirinta na yi wa sama da matasa 1,300 afuwa, wadanda aka fi sani da ‘yan daba, bayan sun amince su mika makamai tare da daina aikata tashin hankali da sauran ayyukan laifi da ke barazana ga zaman lafiya a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen taron kwana ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin ƙungiyoyin matasan da suka tuba, ƙarƙashin shirin Safe Corridor Project, a Kano.
Gwamnatin Kano Ta Raba Takin Zamani Ga Manoma a Gwarzo
Gwamnan, wanda Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Abdullahi Waiya, ya wakilta, ya ce gwamnati za ta tallafa wajen gyara rayuwar matasan da suka tuba tare da mayar da su cikin al’umma ta hanyar shirye-shiryen bunƙasa sana’o’i domin su dogara da kansu.
Ya bayyana cewa wannan shiri na neman bai wa matasan damar barin dabi’u marasa kyau tare da zama masu amfani ga al’umma.
“Shirin Safe Corridor Project wani tsari ne mai zaman kansa da aka kirkiro domin magance ƙalubalen tsaro da tashin hankalin matasa a Kano. Shirin na haɗa da tantancewa, bincike, da gyara halayyar matasan da suka tuba, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro,” in ji shi.
Gwamnatin Kano Ta Kaddamar da Yashe Magudanan Ruwa a Kurna
Gwamnan ya jaddada cewa shirin ba na siyasa ba ne, sai dai kawai don magance matsalar ‘yan daba da sauran munanan dabi’u.
A ƙarƙashin shirin, za a yi wa kowanne mahalarta rajista da bincike ta hannun hukumomin tsaro domin t