Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      I’ll dress elegantly for a week, lady vows as Kano women storm markets

      March 29, 2025

      Dr. Abdullahi Umar Ganduje’s Legacy of Progress and Excellence

      December 25, 2024

      The rise and fall of Faruk Lawan: A lesson in power and intrigues

      December 17, 2024

      Will The Axing of Zakirai Make Education Great In Kano

      December 17, 2024

      Harmattan Brings Boom to Tea, Noodle, Bean Cake Sellers in Kano

      December 15, 2024
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      Fire Guts 45 Houses, 35 Silos in Batakashi Village Jigawa

      April 13, 2025

      Fake Charity Organization Allegedly Dupes Kano Residents

      April 6, 2025

      Chidari Urges Constituents to Uphold Islamic Values

      March 30, 2025

      Kano Lawmaker Provides Ramadan Support to Constituents

      March 16, 2025

      Nigerian Delegation Heads to Vatican for Pope Francis’ Funeral

      April 25, 2025

      Inaugural Flight a Testament to FG, States Partnership – Minister

      April 23, 2025

      Akwa Ibom Gov Flags Off Section 3B of Lagos-Calabar Highway

      April 18, 2025

      Revamped Cooperative Sector to Empower Nigerians – Minister

      April 18, 2025

      Renowned Philanthropist Mrs. Maryam Imoke Yanah Recieves Warrior of Hope Award

      April 27, 2025

      Minister Woos French Investors with Nigeria’s Economic Reforms

      April 11, 2025

      Nigeria, Saudi Arabia Strengthen Anti-Drug Efforts

      April 9, 2025

      Info Minister Leads Delegation to US Broadcasters Conference

      April 7, 2025

      Kano Govt Bans Live Political Programs to Promote Peace

      May 8, 2025

      Governor Namadi Approves Minor Cabinet Reshuffle

      May 6, 2025

      When Stars Align: President Tinubu’s Visit to Katsina

      May 6, 2025

      CDA BUK Hosts 5th International Conference on Drylands

      May 5, 2025
    • Politics

      Kwankwasiyya Ideology Dead In Kano Says Minister Ata

      May 7, 2025

      Just In: PDP Loses Another Governor: Delta’s Oborevwori Joins APC

      April 23, 2025

      Ganduje Inaugurates APC France, Drums support for Tinubu

      April 21, 2025

      No Vacancy For Number One Seat- Jigawa Sen Tells Contenders

      April 15, 2025

      Nigerians Abroad Back Seyi Tinubu for Lagos State Governor

      April 14, 2025
    • Conflict

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025

      El-Rufai Defends Najaatu Muhammad Against Ribadus Denials

      February 5, 2025

      Tinubu’s Corruption Saga: Najaatu-Ribadu Feud Takes Center Stage

      February 5, 2025

      Kano Inaugurates Committee to Investigate Rimin Zakara Dispute

      February 3, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Murtala Sule Garo ya taya Alummar Musulmi Murnar Bikin Sallah

      March 31, 2025

      Gwamnatin Kano zata Sabuntawa Ma’aikatan Shara Kayan Aiki

      March 18, 2025

      Alummar Gwarzo Sun Yi Fitar Dango Don Tarbar Sabon Hakimin Su

      March 17, 2025

      Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Biliyan 16

      March 15, 2025

      KH Gwarzo Ta Kafa Kwamitin Rijiyoyin Burtsatsai Da na Kudin Shiga

      March 12, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Health

    An Bukaci Al’umma Da Su Fito Gwajin Hawan Jini da Ciwon Suga

    EditorBy EditorOctober 31, 2024Updated:October 31, 2024No Comments3 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    IMG 20241030 WA0182

    Yayin da aka fara aiwatar da Shirin Gangamin Mutane Miliyan Goma a faɗin wannan ƙasa, an buƙaci al’ummar jihar Kano da su fito domin yi musu gwajin hawan jini da ciwon siga.

    Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kira yayin fara gudanar da shirin gwajin hawan jini da ciwon suga a harabar Hukumar Samar da Magunguna da Kayayyaki ta Jiha (DMCSA).IMG 20241030 WA0180

    Shirin Mai taken Gangamin Mutane Miliyan Goma ya mayar da hankali ne ga cututtuka marasa yaɗuwa, musamman hawan jini da ciwon siga, waɗanda ke taka rawa wajen haifar da cututtuka da mace-mace a Najeriya,

    Ad 4

    Hakan ta sa Zauren Kwamishinonin Lafiya na Najeriya ya yi damarar magance matsalar, wanda gangami ne na ƙasa baki ɗaya da ke da ƙudirin yi wa ‘yan Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya na Abuja, tsawon mako guda.IMG 20241030 WA0181

    Daga cikin manufofin shirin akwai yi wa al’ummar Najeriya miliyan goma gwajin hawan jini da ciwon siga, da haɗa sakamakon da aka tabbatar da hanyoyin samun waraka, da samar da magunguna na ƙaramin zango daidai da tsarin da ya dace, da ƙara wayar da kan al’umma da ilimantar da su game da hawan jini da ciwon siga, da ilimantar da al’umma game da abincin da za su rinƙa ci, da motsa jiki, da kaucewa shan taba, da sauransu.

    Dakta Labaran ya buƙaci mutane da su shigo a dama da su a cikin wannan aiki don tabbatar da yadda matakin lafiyarsu yake, ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da waɗannan cututtuka za a ba su magani kyauta ko kuma a tura su asibiti mafi kusa domin a ci gaba da kula da lafiyarsu idan an fahimci larurar tasa babba ce.

    Ad 3

    Kwamishinan ya shawarci jama’a da su kai iyalansu wuraren da aka ware don yin gwajin a cibiyoyin da aka tanada don yin aikin kyauta har tsawon mako guda a faɗin jihar Kano, yana mai fatan yi wa mutane miliyan ɗaya a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

    Ya ce “Aikin, wanda zai lashe kusan Naira miliyan 800, babba ne. Saboda haka, mutane, daga kan ɗan shekara 20 zuwa sama, na buƙatar su yi cikakken amfani da wannan dama wajen yin gwajin waɗannan cututtuka masu hallakarwa.

    Waɗanda aka samu da ɗaya ko kuma duka cututtukan kada su razana, maimakon haka su gode wa Allah saboda an gano wata cuta da ta ɓuya a jikinsu, domin su nemi waraka.

    Dakta Labaran ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake nuna damuwa da lafiyar al’ummar jihar Kano a kowane lokaci, ya kuma jinjina wa ƙungiyoyi masu tallafa wa fannin lafiya da sauran masu ruwa da tsaki bisa yadda suke bayar da gudummawa wajen ci gaban lafiya.

     

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Gombe Polio Campaign Overcomes Initial Resistance, Achieves Success

    April 29, 2025

    Kano Flags Off Polio Vaccination Campaign, Warns Against Resistance

    April 27, 2025

    KSrelief Performs 28 Cochlear Implant Surgeries in Kenya

    April 25, 2025

    Kano Targets 4.5 Million Children in Polio Vaccination Campaign

    April 23, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    Kano Approves N2bn Compensation for Road Project Affected Communities

    May 8, 2025

    Kano Seals 2 Warehouse Causing Environmental Nuisance

    May 8, 2025

    Kano Govt Bans Live Political Programs to Promote Peace

    May 8, 2025

    Kano Govt Urges Private Schools to Adhere to Regulations

    May 8, 2025
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.