An kama shugaban makaranta da wata malamai mata a garin Thane da ke jihar Maharashta ta ƙasar Indiya.
Ana zargin mutanen biyu ne da cire wa ɗalibai mata kaya domin duba ko suna jinin al’ada ko kuma a’a, bayan ganin ɗishi-ɗishin jini a bangon ban-ɗaki.
Ƴansanda sun ɗauki matakin ne bayan mahaifiyar ɗaya daga cikin ɗaliban kimanin 15 ta shigar da koke kan lamarin.
Menstrual Hygiene Day:NAWOJ YOSPIS Sensitizes Kano Students
Makarantar na ƙunshe ne da ɗalibai kimanin 600, wadanda ke karatu daga matakin nazare zuwa sakandare.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Talata a gundumar Shahpur na birnin Thane.
A ranar Laraba iyayen yara sun yi zanga-zanga a harabar makarantar sannan suka buƙaci gwamnatin yankin ta hukunta masu hannu a lamarin.
Bayan haka ne ƴansanda suka sanya ido kan mutum 8 da ake zargi, inda a yanzu suka kama shugaban makarantar da kuma wata malama.
KanSLAM Says it is Commited to Enhanced Menstrual Hygiene
Ƴansandan na zargin mutanen da cin zarafi da kuma keta mutuncin ɗaliban kamar yadda yake ƙunshe a doka.
Bayanin ƴansanda ya nuna cewa lamarin ya faru ne tsakankanin ƙarfe 10 zuwa 12 na rana a ranar 8 ga wannan wata na Yuli, lokacin da shugaban makarantar ya tara yara mata ɗalibai na makarantar su 125 a ɗakin taro na makarantar.
Daga nan ne aka kunna masu bidiyon jinin da aka gani a ban-ɗaki, sannan aka tuhume su da ɓata bangon da jinin al’ada.
Bayanin ya ce daga nan ne aka umarci malamai mata na makarantar su tafi da ɗaliban ban-ɗaki su cire musu kaya domin gano waɗanda ke jinin al’ada.
Lamarin, a cewar bayanin ya girgiza ɗaliban.
Wasu daga cikin iyayen sun ce yaransu sun ƙi zuwa makaranta sanadiyyar kaduwar da suka yi.
BBC HAUSA