Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi wani korafi dake neman ta shiga tsakani a kan abin da aka bayyana a matsayin tsawaita wa’adin aiki ga wasu manyan jami’an gwamnati ta hanyar amfani da doka mai lamba 1 ta shekarar 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar.
A cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 6, ga watan Janairu 2025, Sani Usman DanAbdullo, Esq, Daraktan gudanarwa na hukumar yaki da cutar kanjamau ta jihar Kano (KSACA), ya bukaci majalisar da ta dauki mataki domin kare tsarin mulki da hana karya dokar amfani da ikon zartarwa
Jaridar Kadaura24 ta ruwaito wasikar mai dauke da kwanan wata 6 ga watan Junairu 2025 an aika ta zuwa ga shugaban majalisar, Right Honourable Jibrin Ismail Falgore, da kuma shugaban kwamitin majalisar kan karbar korafin jama’a.
Takardar koken ta nuna cewa dokar zartarwar da aka bayar a ranar 1 ga Janairu, 2025, ta yi zargin tsawaita wa’adin aiki na shekaru 2 ga jami’ai da suka hada da shugaban ma’aikata, magatakardar majalisar, wasu jami’an shari’a, da ma’aikatan sashen lafiya .
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da tsawaita wa’adin aiki na tsawon shekaru biyu ga shugaban ma’aikatan gwamnati, da wasu manyan sakatarorin gwamnati, da manyan ma’aikatan gwamnati, daga ranar 31 ga Disamba, 2024.
Gwamnan Kano ya roki gwamnatin tarayya ta rage kudin Aikin Hajjin 2025
A cewar gwamnan, ya yi amfani da dokar zartarwar mai lamba 1 da sashe na 5 (2) da sashe na 208 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 wajen tabbatar da karin wa’adin shekaru biyun ga wadancan mutane.
Wannan matakin, a cewar koken, ya saba wa dokokin da Majalisar ta kafa, da suka hada da dokar fansho ta jihar Kano (gyara mai lamba 5) ta 2024, wadda ta ce ma’aikaci zai yi ritaya ne idan ya cika shekaru 60 da haihuwa ko kuma ya cika shekaru 35 da fara aiki .
Takardar koken ta ce tsawaita wa’adin aikin ga wadanda can ma’aikata ya sabawa Doka .
Mai shigar da karar ya ci gaba da cewa masana shari’a da kundin tsarin mulkin Nigeria sun fassara cewa bai kamata wacce doka da gwamnan Kano yayi amfani da ita ta danne dokar da majalisar ta gyara ba.
Da ɗumi-ɗumi: Ogan Ɓoye ya nada sabbin hadimai 60 a karamar hukumar Nassarawa.
Takardar ta kuma yi watsi da dogaron da gwamnan ya yi kan akidar wajabcin tabbatar da wannan odar, inda ta bayyana shi a matsayin wanda ba shi da tushe a cikin doka da kuma tsarin mulki.
Mai shigar da korafin ya bukaci Majalisar da ta yi aiki da ayyukanta na sa ido domin rusa tsarin zartarwa tare da hana abin da ya kira wani lamari mai hadari da zai iya gurgunta tsarin aikin gwamnati a jihar
KADAURA