Close Menu
PARADIGM NEWS
    Facebook X (Twitter) Instagram
    • Home
    • Privacy Policy
    Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
    PARADIGM NEWS
    • Home
    • Features

      I’ll dress elegantly for a week, lady vows as Kano women storm markets

      March 29, 2025

      Dr. Abdullahi Umar Ganduje’s Legacy of Progress and Excellence

      December 25, 2024

      The rise and fall of Faruk Lawan: A lesson in power and intrigues

      December 17, 2024

      Will The Axing of Zakirai Make Education Great In Kano

      December 17, 2024

      Harmattan Brings Boom to Tea, Noodle, Bean Cake Sellers in Kano

      December 15, 2024
    • News
      1. Local
      2. National
      3. International
      4. View All

      One Confirmed Dead, Woman Rescued Alive in Kano Well Accidents

      June 30, 2025

      Philanthropist Donates 600 Bags of Maize To Insurgency Victims

      June 27, 2025

      Kazaure NDLEA Holds Road Show to Combat Drug Abuse Illicit, Trafficking

      June 26, 2025

      MfLGCA, PACE Partner for Grassroots Governance Reforms

      June 23, 2025

      NAPTIP, NARTO Unveil Strategic Collaboration to Disrupt Trafficking

      July 2, 2025

      Presidency Debunks Rumours of SGF Akume’s Removal

      June 30, 2025

      President Tinubu Embarks on Diplomatic Visit to Saint Lucia, Brazil

      June 28, 2025

      Efficient Civil Service Key to National Development – Alake

      June 25, 2025

      Brussels: Nigeria’s Digital Blueprint Takes Global Stage at IGF

      June 27, 2025

      Nigeria, S/Arabia Sign Agreement to Tackle Smuggling, Boost Trade

      June 27, 2025

      Nigeria Showcases Bold Health Reforms at BRICS, Pledges $200M

      June 19, 2025

      KSrelief to Tackle Nigeria’s Water Shortage with 78 Solar Boreholes

      June 19, 2025

      Jigawa Renames Ministry, Approves N19.6B for 560 Mass Housing

      June 27, 2025

      KNSG Declares Thursday, Work-Free Day to Mark Islamic New Year

      June 25, 2025

      Gov. Yusuf Vows to Empower Media Practitioners in Kano

      June 25, 2025

      Gov Yusuf Condemns Killing of Two Kano Indigenes in Makurdi

      June 24, 2025
    • Politics

      Kano APC Coalition Submits letter to Natl Ag. Chairman, Demands Dissolution Of State Leadership

      July 2, 2025

      “Kwankwaso Remains Our Focus” – Jigawa NNPP Leader

      June 28, 2025

      Breaking: APC National Chairman Abdullahi Ganduje Resigns

      June 27, 2025

      Rivers: Tinubu Brokers Peace in Closed-Door Abuja Meeting

      June 27, 2025

      Radda Dismisses VP Ambition Rumors, Reaffirms Commitment to Katsina

      June 27, 2025
    • Conflict

      Kadpoly Retiree faults Committee, Demolition Of Property

      March 27, 2025

      President Tinubu Declares State of Emergency in Rivers State

      March 18, 2025

      El-Rufai Defends Najaatu Muhammad Against Ribadus Denials

      February 5, 2025

      Tinubu’s Corruption Saga: Najaatu-Ribadu Feud Takes Center Stage

      February 5, 2025

      Kano Inaugurates Committee to Investigate Rimin Zakara Dispute

      February 3, 2025
    • More
      • Analysis
      • Business
      • Crime
      • Cultural events
      • Economy
      • Education
      • Editorial
      • Entertainment
      • Environment
      • Fashion
      • Health
      • Lifestyle
      • Personality profile
      • Science
      • Sports
      • Technology
    • Hausa

      Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

      July 3, 2025

      Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

      July 3, 2025

      An kwantar da Tsohon Shugaban Kasa Buhari a ICU a Landan

      July 2, 2025

      Sanata David Mark ya fice daga jam’iyyar PDP

      July 2, 2025

      Kano Za Ta Hada Gwiwa da Kungiyoyi Don Rage Talauci — Kibiya

      July 2, 2025
    Subscribe
    PARADIGM NEWS
    Hausa

    Finafinan Kannywood Biyar Da Suka fi Shahara a Shekarar 2024

    EditorBy EditorDecember 26, 2024Updated:December 26, 2024No Comments6 Mins Read
    Facebook Twitter Telegram WhatsApp
    1735203657485

    A Kannywood, ana ta samun sauye-sauye, musamman a ɓangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hanƙoron shiga manhajojin duniya ka’in da na’in.

    A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, waɗanda suka ƙayatar da masu kallo.

    Tun bayan komawa ɗora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana’antar ta fara durƙusawa.

    Ad 4

    Wannan ya sa BBC ta tankaɗe, ta rairaye, sannan ta zaƙulo wasu finafinai da suka yi tashe a shekarar 2024.

    Sai dai finafinan na bana dukka masu dogon zango ne, wanda hakan ke nuna yadda masana’antar ta sauya, da kuma hanyar da ta dosa domin ɗorewarta.

    Da farko da aka fara finafinai masu zango, an yi tunanin ƙananan masu shirya fim ne kawai suka yi, su ɗora a YouTube, har ma wasu suke ganin ba su da inganci. Amma yanzu an wayi gari manyan furodusoshin Kannywood sun shiga ana damawa da su.

    Ad 3

    Daga cikin finafinan da muka zaƙulo, akwai waɗanda ba a shekarar 2024 aka fara su, amma sun ja hankalin mutane a shekarar.

    Ga yadda jerin fina-finan ya kasance a cikin shekarar gwargwadon nazarin da muka yi:

    Labarina

    Labarina fim ne mai dogon zango na fitaccen darakta, Malam Aminu Saira, wanda sunansa ya riga ya yi amo, ta yadda ba ya buƙatar gabatarwa ga dukkan masu kallon finafinan Hausa.

    Fim ne mai tsari shigen labarin ‘Dare dubu da ɗaya’, inda daga wannan labarin za a shiga wani labarin daban, wanda a cewar daraktan, hakan zai sa fim ɗin ya daɗe ba tare da ya salance ba saboda ba labari ɗaya ba ne.

    A shekarar 2020 aka fara fim ɗin da labarin Sumayya wato Nafisa Abdullahi wadda daga baya ta rikiɗe ta koma Fati Washa, wanda a ƙarshen zango na bakwai aka dakata da labarin Sumayya, aka tafi hutu.

    Amma yanzu labarin ya koma na Alhaji Mainasara wato Sadiq Sani Sadiq, wanda aka fara daga zango na takwas, kuma yanzu haka ana zango na 11.

    Labari ne kan yadda Alhaji Mainasara ya ɓatar da kama, ya fito a matsayin talaka domin samun soyayya ta gaskiya bayan wahalar da ya sha a farko, inda ya haɗu da Jamila wato Amina Uba Hassan, ya nuna mata ƙauna.

    Daga bisani ya tura mata direbansa da sunan yana da arziki, ita kuma ta amince da shi, maimakon Mainasara.

    Ana cikin haka ita kuma ƙawarata, Maryam wato Fatima Hussaini ta amince za ta aure shi a haka. Bayan aure komai ya fito fili.

    The Kannywood Icon: Abba El-Mustapha

    Amma daga baya matsalar jina da ta sa Maryam ba za ta haihu da shi ba ta sa aura Dokta Asiya wato Diamond Zahra.

    Fim ɗin ya fitar da jarumai mata waɗanda yanzu ake yi da su a masana’antar irin su Firdausi Yahaya da Fatima Hussaini da Amina Uba Hassan da sauransu.

    Yawancin fitowar fim na mako na samu masu kallo sama da miliyan 1.

    1735203778156

    Manyan Mata

    Fim ɗin Manyan Mata shi ma ba a shekarar 2024 aka fara ba, amma yana ci gaba da jan masu kallo.

    Fim ne da ya tara manyan jarumai masu yawan gaske, wanda za a iya cewa ba a saba ganin hakan ba.

    Furodusa Abdul Amart Maikwashewa ne ya shirya, kuma ya ɗauki nauyi, sannan Sadiq N. Mafia ya fara bayar da umarni, daga baya Ali Gumzak ya cigaba.

    A fim ɗin an nuna yadda wasu mata suke shan wahala a gidajen miji da ƴan gudun hijira da sauran mata talaka, da yadda wasu suke amfani da damar da suke da ita cin zarafinsu.

    Sannan a gefe guda kuma, akwai mata biyu wato Laila (Hadiza Gabon) da Nadia wato Aisha Tsamiya wadda aka maye da Rabiatu Ƙafur da suke ƙoƙarin ƙwato ƴancin mata da ƙungiyarsu ta ‘Manyan Mata’, tare da ƙoƙarin nuna amfanin ilimin ƴaƴa mata.

    Star Of Kannywood: Sani Danjas Rise To Stardom Within Few Years

    Yanzu dai kallo ya koma sama, bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu.

    Kusan duk wani babban jarumi a Kannywood suna cikin fim ɗin, har da waɗanda aka daɗe ba a ji ɗuriyarsu ba.

    Yanzu haka furodusan shirin Abdul Amart ya sanar da cewa suna gab da kammala ɗaukar zango na huɗu na shirin.

    Yawancin fitowar fim ɗin a mako yana samun masu kallo kusan 500,000.

    1735203760330

    Gidan Sarauta

    Gidan Sarauta na cikin finafinai masu dogon zango na furodusa Abubakar Bashir Maishadda, wanda yake jan hankalin masu kallo.

    An fara fitar da fim ɗin ne a ranar 5 Nuwamban 2023, kuma yanzu ana zango na uku, kuma jarumi Umar M. Shareef da jaruma Mommee Gombe ne suke jan fim tare da taimakon Garzali Miko da Aisha Najamu.

    Ali Nuhu da Hadizan Saima da Yakubu Mohammad da Rabiu Rikadawa da Abale duk suna cikin fim ɗin.

    An gina fim ɗin ne a kan Umar M. Shareef wanda ya fito a yarima mai jiran gado ya faɗa soyayya da ƴar talaka, Bintu (Momme Gombe) amma bai bayyana ba, daga ƙaninsa ya riga shi aurenta.

    Zainab Indomie: Beauty, Talent, and Resilience in Kannywood

    Amma sai aka gane akwai wani abu a tsakaninsu, wanda hakan ya sa ƙanin ya sake ta, shi kuma ya aura. Wannan ya sa aka yi fushi da shi, aka ba shi zaɓin ko dai Bintu ko sarauta, inda ya zaɓi matarsa, ya haƙura da sarautar.

    Daga bisani shi ma Garzali ya hango yarinyar Tafida, wato Badariyya (Firdausi Yahaya) inda ya faɗa kogin ƙauna, amma yana tsoron shiga halin da yayansa yake ciki.

    Ali Nuhu ya ba da umarnin fim ɗin, wanda dukkan jaruman suka dage wajen fitar da labarin fes.

    1735203748174

    Garwashi

    Garwashi fim ne da aka fara fitarwa a ranar 12 ga watan Agustan 2024 a YouTube.

    An shirya fim ne a kan ƙalubalen da matan da mazajansu suka rasu suke fuskanta daga wurin ƴanuwa da mutanen gari.

    Jarumar da ja shirin, Asma’u wato Firdausi Yahaya tana shan fama daga dangin mijinta da ƴanuwanta da ma wuraren da take aiki.

    Rahama Ibrahim Sadau: A Star in Multiple Film Industries

    Fitacciyar marubuciya Fauziyya D. Suleiman ce ta tsara labarin, sannan fitaccen darakta Yaseen Auwal ya ba da umarni.

    Fim ya ɗauki hankalin masu kallo sosai cikin ƙankanin lokaci musamman ganin yadda jarumar take shan wahala.

    1735203730164

    Allura cikin ruwa

    Fim ne da aka shirya kan Na’ima wato Rukky Ali, wadda marainiya ce, wadda aka tsinta bayan an kashe mahaifiyarta, wato Firdausi Yahaya.

    Daga baya maza irin su Maina wato Yakubu Mohammad wadda take wa kallon ƙanin mahaifi , da Alhaji Hadi wato Sani Danja da Dr Hashim wato Adam A. Zango da Sadiq wato Isa Ferozhkan wanda suka daɗe suna soyayya, duk suka nuna sha’awar aurenta.

    The Rise of Hadiza Gabon: From Gabon to Kannywood Stardom

    Daga baya aka gano ashe tana da tarin dukiya da aka rasu aka bar mata.

    Saboda soyayyarta ce Maina ya fallasa cewa Tijjani Faraga ba mahaifinta ba ne, don haka ya ce babu laifi don ya aure ta.

    Kamfanin 2Effects ne ya ɗauki nauyin shirin, sannan Yakubu Mohammed ya ba da umarni. Yanzu ana zango na biyu.

    1735203711113

    BBC HAUSA

     

     

    Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram WhatsApp

    Related Posts

    Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

    July 3, 2025

    Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

    July 3, 2025

    An kwantar da Tsohon Shugaban Kasa Buhari a ICU a Landan

    July 2, 2025

    Sanata David Mark ya fice daga jam’iyyar PDP

    July 2, 2025
    Add A Comment
    Leave A Reply Cancel Reply

    Editors Picks

    Sekure Ya Tallafa wa Sabbin Jami’an Kashe Gobara da N480,000

    July 3, 2025

    Wutar Lantarki Ginshikin Cigaban Ilimi da Tattalin Arziki-Gwamna

    July 3, 2025

    Barau FC Arrives Asaba for NNL, Targets NPFL Promotion

    July 3, 2025

    Edu Reform in Focus as Kano Partners PLANE for MTSS Workshop

    July 3, 2025
    Hajaj Albait 2
    © 2025 PARADIGM NEWS
    • Home
    • Privacy Policy

    Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.