Majalisar Dokokin jihar Kano tayi watsi da rahotanin dake yawo na cewar tana kauracewa Zaman Majalisar ne sakamakon barazanar tsaro gami da dambarwar masarauta a jihar.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano Mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dokokin jihar Kano Kamaluddeen Sani Shawai ya ce wannan rahoton babu kanshin gaskiya a ciki.

Yace majalisar tana da damar tafiya hutu kamar yadda ta Saba Wanda hakan ke ba ‘yan majalisar damar tattuanawa da jama’ar su.

READ ALSO: Mosque Explosion:KNHA Urges Government to Assist Victims Families

Kuma wannan wa’adin hutun majalisar zai Kare ne a ranar Sha biyar ga watan da muke ciki inda ‘yan majalisar zasu koma domin cigaba da samar da dokokin da zasu inganta rayuwar Alumma.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version