An bayyana cewa an samu kasuwancin magunguna na jihar Kano, bayan ƙarewar shekaru takwas na zangon mulki na biyu na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a cikin yanayi mara daɗi.
Commissioner for Health Vows to Revamp Pharmaceutical Industry
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka yayin da yake karɓar shugabannin Кungiyar Masu Haɗa Magunguna da Sarrafa su ta Najeriya, reshen jihar Kano, da suka ziyarci shi a ofishinsa.
Ya koka da cewa sun samu kasuwar magani, musamman Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti (DMCSA), hukuma ɗaya tilo da gwamnati ta amince ta samar wa asibitoci magunguna masu inganci da sauƙi, a durƙushe tana buƙatar ɗauki.
Kwamishinan Lafiya Ya Yabawa K/H Uku Akan Rigakafin Shan Inna
Dakta Labaran ya yi farin ciki da samun dunƙulalliyar kasuwar hada-hadar magunguna a Ɗangwauro kasancewar abubuwa sun fara dawowa daidai, ya ƙara da cewa abin da kawai ya rage shi ne tilasta amfani da kasuwar yadda ya kamata domin a tsaftace kasuwancin magunguna a jihar.
Kwamishinan ya ce sirrin da ke tattare da samun nasarar ayyukan samar da magunguna a Kano ta biyo bayan neman shawarar ƙwararru kan harkokin magunguna da yake yi game da duk wani abu da ya shafi harkar kafin ya tura wa Gwamna Abba Kabir Yusuf.
K/H Garun Malam Ta Umarci ‘Yan Kasuwar Kwanar Gafan Da Su Tashi Cikin Kwanaki 7
Ya bayyana cewa, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf tana yin ayyukan da take yi ne domin al’umma, yana mai shawartar masu kasuwancin magani da su yi taka-tsantsan da jin tsoron Allah yayin da suke gudanar da ayyukansu, domin za a iya sake canja tare da sarrafa maganin da wa’adinsa ya ƙare a sake mayar da su kasuwa, yana mai yarda da cewa mutum mai tsoron Allah bai zai yi irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.
Dakta Labaran ya ce ya yi farin ciki sosai da ɗaukar nauyin ɗalibai zuwa ƙasar Indiya su yi karatun haɗa magunguna da sarrafa su a lokacin da yake kwamishina a tsakanin shekarar 2011 da 2015, ya ce a lokacin ‘yan Kano masu rajista a wannan ilimin 51 ne kawai, wanda hakan ya sa Gwamna Kwankwaso ya umarce shi ya tantance mutum 100 aka tura su Indiya, da mafi yawansu yanzu haka suna hidimta wa Kano.
Da yake jawabi tun da fari, Shugaban Кungiyar, Famasis Mustafa Umar ya ce sun zo ma’aikatar ne domin su nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin kwamishinan na kawo sauyi a sashin lafiya na jihar nan.
Ya nuna farin cikinsa da cewa dawowar kwamishina ta zo a lokacin da ya dace saboda masu ilimin haɗa magunguna da sarrafa su na jihar Kano suna cikin damuwa mai tsanani game da makomar DMCSA, amma yanzu sun samu nutsuwa saboda abubuwa sun fara dawowa daidai da ta kai yanzu ake samun magani kashi 96 cikin 100 a asibitoci idan an kwatanta da baya da ake samun kaso 30 kawai.
Shugaban ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa naɗa ɗaya daga cikinsu, Famasis Aminu Bashir a matsayin Babban Sakatare, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin jihar Kano, yana mai tabbatar da cewa babban sakataren zai yi aiki tuƙuru wajen ci gaban aikin gwamnati duba da ƙwazo da jajircewarsa a aiki.
Daga nan sai ya sanar da kwamishinan cewa a watan Nuwamba, na wannan shekarar, jihar Kano za ta karɓi baƙuncin taron Кungiyar Masu Samar da Magunguna da Sarrafa su da ake sa ran ‘ya’yan ƙungiyar dubu uku zuwa dubu biyar za su ziyarci Kano, inda ya nemi gudummawar gwamnati.