Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗu, ya nuna takaicinsa kan wasu zarge zarge, da shugaban mulkin sojin Nijar Janar Abdulrahman Tchiani ya yi yayin hirarsa da kafar talabijin ɗin kasar ranar Laraba.
Minister receives Kaduna Abducted Journalists salutes NSA
Shi dai Janar Tchiani ya zargi Najeriya da ba ƙasar Faransa hadin kai wajen ba ƴan bindiga mafaka da kuma ƙoƙarin kafa sansani a arewacin Najeriya, don shirya yadda za su farwa ƙasarsa.
To sai dai a hirarsa da BBC Hausa, mai ba Shugaban Najeriyar shawara kan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya ce dukkan wadannan maganganu basu da tushe, ballantana makama, kana Najeriya ba za ta taba yi wa Nijar zagon kasa ko ta bari wata masifa ta auka mata ba.
Northern Star Youth Initiative Kicks Against Nigeria’s Romance With France
Ya ce ‘’Ko Ingila da ta mulki Najeriya ba ta taɓa kawo sojoojinta kasarmu ba, sai da suka yi dukkan mai yiwuwa muka ƙi yarda sannan suka kai su Nijar din, ita kuma ta yadda ta karɓa, haka ita ma Faransar da ta mulke su ta so ta kawo mana sojojinta, muka ce ba mu amince ba, me ya sa sai yanzu za mu sake shawara?
Sai dai a cewarsa ya kamata shugabannin Nijar din su fahimci cewa don kawai suna da wata matsala da Faransa, ba shi ke nufin cewa dole ne ita ma Najeriya ta yi zaman doya da manja da kasar ba.
Wani babban zargi da shugaban Nijar din ya yi wa Najeria shine na ba wa sojojin Faransar sansani a wani tsbiri a jihar Borno, daf da tafkin Chadi, da ake kira Canada, inda Faransar ta jibge sojojinta a wurin, har ma ya kama sunan shi Nuhu Ribadu, ya ce ya san duk wannan magana
Sai dai a hirarsa da BBC, Nuhu Ribadu, ya ce ‘’Ba shakka shi shugaban Nijar ya san Najeriya sosai, amma ina so ku a matsayinku na ƴan jarida, ku je wuraren da ya faɗa ku duba da kanku, ko ku tambayi mazauna wuraren ko akwai wasu baƙi ma, ballantana sojojin wasu ƙasashen’’
‘’Su shugabannin mulkin sojin Nijar ya kamata su fahimci cewa mu Najeriya ba matsala bane gare su, waɗannan yan ta’adda da duka muke yaki da su sune matsalarmu, ya kamata mu tunkare su tare’’ in ji mai ba wa shugaban Najeriyar shawara kan harkokin tsaro.
Ya kara da cewa ‘’Don Allah shugabannin Nijar su sake dubawa, ba yadda za a yi a ce Najeriya ce za ta taimaka wa yan ta’adda su yake ta, kuma ya kamata su san cewa idan sun kori Faransa sun kuma sake kawo wasu, to sun canja matsalar ne kawai, bai kamata su kawo wasu ba, duk wanda ya zo maka da farko zai zo a matsayin aboki ne, ko lokacin da suka kawo Faransa mun ba su wannan shawarar, amma basu ɗauka ba’’
Ya ce Najeriya ba ta da niyyar nesanta kanta da maƙwabciyar ta ta, domin kasashen biyu da al’umominsu yan uwan juna ne, don haka kamata ya yi su hada kai su yi aiki tare, don ci gaban al’umominsu.
A baya bayan nan ma sai da ministan harkokin wajen Nijar ɗin ya gayyaci jami’a mai kula da harkokin diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar, don ta je ta yi bayani kan zargin da suke yi wa Najeriyar na hada kai da wasu kasashen Turai wajen shirya mata manaƙisa.
Ministan ya yi zargi cewa, duk da irin na-mijin ƙoƙarin da Nijar ke ta yi na ganin ta kyautata dangantaka da daɗaɗɗiyar aminiya ko ma abokiyar tagwaitakar ta ta, watau Najeriya, amma ƙasar bata hakura ba, inda take ci gaba da haɗa kai da wasu manyan ƙasashen duniya da jami’an tsohuwar gwamnatin Bazoum da ke zaman mafaka a Najeryar ake ci gaba da kitsa yadda za a jefa ƙasar cikin hargitsi.
Zarge zargen da shugaban Nijar ya yi wa Najeriya
Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daɗewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi.
‘’Wasu manyan ‘yanta’adda da muka kama, sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Najeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba da ke jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi a Najeriya sansanin horas da mayaƙan Lakurawa’’, in ji shugaban na Nijar.
Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadin sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.
Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Najeriya na sane, ba su yarda da maganar ‘yan bindigar ba.
Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da masaniya game da wannan batu.
Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabtaka.
Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bai wa Faransa damar kafa sansanoni a ƙasashen domin horas da ‘yanta’adda da niyyar yaƙar Nijar.
A baya-bayan nan dai dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami, ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Najeriya da shirya mata maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.
BBC HAUSA