Shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano, Alhaji Abba, ya jaddada kudirinsa na dakile ayyukan rashin da’a da ke yaduwa a kafafen sada zumunta na zamani, musamman a tsakanin matasa.
A yau, hukumar ta samu nasarar cafke wasu matasa guda hudu da ake zargi da amfani da manhajar TikTok wajen yada abubuwan da suka saba da tarbiyya da kuma kalamai marasa ma’ana.
Wadanda aka kama sun hada da Hafsa Hamisu (Zoom Zoom), Usman Majidadi (Majidadi), Sumayya Muhammad (Summy Beby), da Usman Ibrahim (Maikalar Kudi).
“From Influencer to Convict”: Murja Kunya Jailed for Naira Abuse
Lamarin ya sabawa dokokin hukumar, wanda hakan ya sanya aka gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukunci bisa abinda suka aikata.
Lauyan masu kara, Barr. Garzali Maigari Bichi, ya karanta tuhume-tuhumen da ake musu, inda dukkan wadanda ake zargin suka amsa laifukansu nan take.
Kotun Majistiri dake no man’s land Karkashin jagorancin Mai shari’a Halima Wali ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga Yuni, 2025, tare da bada umarnin a cigaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’ar.
Naira Abuse: EFCC Set to Charge TikTok Influencer Murja Kunya
A baya-bayan nan, hukumar ta kai irin wadannan matasa gaban kotu, inda aka yanke musu hukuncin daurin shekara guda ko zabin biyan tarar Naira dubu dari (₦100,000). Kotun ta kuma gindaya sharadin cewa kada su sake maimaita irin wannan laifi, tare da wanda zai karbe su daga gidan yari.
Wannan yunkuri na daga cikin kokarin da hukumar ke yi na tsawon lokaci domin tsaftace harkokin kafafen sada zumunta a jihar Kano. Hukumar na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa abubuwan da ke yaduwa sun dace da al’ada da kuma koyarwar addinin Musulunci.