Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Barrista Ismael Ahmed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Shirin Gas ɗin CNG na Shugaban Ƙasa Mai lakabin (Presidential Compressed Natural Gas Initiative – PCNGi) a turance.
Sanarwar nadin ta fito ne daga hannun Bayo Onanuga, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, wanda aka rabawa manema labarai.
PCNGI Launches CNG Mobility Framework to Boost National Gas Supply
A matsayinsa na Shugaban shirin, Ismael Ahmed, mai shekaru 45, zai jagoranci aiwatar da shirin PCNGi wanda ke cikin muhimman matakan gwamnatin Tinubu na rage raɗaɗin cire tallafin mai ta hanyar samar da makamashi mai araha, tsafta da dorewa ga al’ummar Najeriya.
Wannan shiri wani muhimmin ɓangare ne na manufofin rage wahala bayan cire tallafin mai, kuma yana da burin ƙarfafa amfani da compressed natural gas (CNG) a matsayin madadin dizel da fetur.
CNG: Kano State, STATA Power Utilities Sign $15 Million MoU
Wane ne Ismael Ahmed?
Ya karanci Shari’a (LL.B) a Jami’ar Abuja inda ya kammala a shekarar 2005
An kira shi zuwa Bar a Najeriya a shekarar 2006
Ya samu digiri na biyu a Harkokin Ƙasashen Duniya, Sadarwa da Diflomasiyya daga Webster University, St. Louis, Missouri, Amurka, a 2008
Ayyukan Gwamnati
Ya kasance Mai Baiwa Shugaba Muhammadu Buhari Shawara na Musamman kan Shirin Tallafi na Ƙasa (NSIP) daga shekarar 2018 zuwa 2022
Nadin Ismael Ahmed na nuna yadda gwamnatin Tinubu ke ƙoƙarin tabbatar da cewa kwararru ne ke jagorantar muhimman shirye-shiryen farfaɗo da tattalin arziki da kuma sauya tsarin makamashi zuwa na zamani.