Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa samun ingantacciyar wutar lantarki ba kawai hidima ba ce, illa kuwa wata muhimmiya ce wajen habaka ilimi, kiwon lafiya, masana’antu da kuma rage talauci.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin bude taron bita kan Kasuwar Lantarki ta Jihohi, Tsarin Tsare-tsaren Albarkatun Wuta da kuma tsarin Plexos Software, wanda Kungiyar Gwamnonin Najeriya tare da UK Nigeria Infrastructure Advisory Facility (UKNiAF) da UK International Development suka shirya a Kano.
Batagari Sun Lalata Layin Wutar Lantarkin Arewacin Nageria-TCN
A jawabin sa wakilin gwamnan, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Abdullahi Musa, ya jinjina wa Gwamnatin Tarayya bisa jajircewar ta wajen magance matsalar wutar lantarki, musamman ta hanyar zartar da sabon Dokar Wutar Lantarki ta 2023.
“Wannan doka ta bude sabon babi ga jihohi, inda yanzu suke da ikon tsara dokoki da gudanar da harkokin samar da wuta, watsawa da rarrabawa a cikin yankunansu,”.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa Jihar Kano na kan gaba wajen aiwatar da sauye-sauyen da suka shafi wutar lantarki, tare da daukar matakai masu karfi don cimma ‘yancin makamashi da dorewar tattalin arziki.
Daya daga cikin wadannan matakai shine kafa Ma’aikatar Wutar Lantarki da Sabbin Makamashi ta Jihar Kano, domin tsara manufofi, karfafa kirkire-kirkire da janyo jarin masu zuba jari a fannin wuta.
Jihohi Sun Fada Duhu Sakamakon Katsewar Layin Wutar Lantarki
Ya kuma bayyana cewa an riga an zartar da Dokar Lantarki ta Jihar Kano, wacce za ta ba da doka da tsarin kafa cikakkiyar kasuwar wutar lantarki a jihar.
“Mun farfado da aikin tashar samar da wutar lantarki ta Hydro da aka dade da watsi da ita, kuma yanzu tana dab da kammaluwa. Wannan aikin zai samar da wuta mai tsafta da dorewa ga al’ummar jihar,”.
Ya jaddada muhimmancin taron, yana mai kira ga mahalarta da su himmatu, su raba ra’ayoyi, su hada kai domin cimma burin samar da ingantacciyar wutar lantarki da ci gaban tattalin arziki, ba a Kano kadai ba, har da sauran jihohi.
Taron ya hada da kwararru daga bangaren makamashi, jami’an gwamnati, abokan ci gaba, da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken sauyi a fannin wutar lantarki a Najeriya.