Zanga-zanga ta ɓarke a kudancin China sakamakon cin zarafin wata ɗaliba ƴar shekara 14 inda mutane ke ta neman a yi mata adalci.
A makon da ya gabata ne wani bidiyo da a ciki wasu sa’annin yarinyar suke zabga mata mari da kuma tilasta mata tsayawa kan gwiwoyinta ya karaɗe shafukan sada zumunta a birnin Jiangyou da ke Lardin Sichuan.
Ƴansanda sun ce yaran da ake zargi da cin zarafin ɗalibar – dukkansu mata ne ƴan shekara 13 da 14 da kuma 15, kuma an tura biyu daga cikinsu makarantu na musamman domin gyara masu tarbiyya.
Bayan da labarin yarinyar ya bazu a shafukan sada zumunta, wasu da dama na ganin an yi sassauci a matakin da aka ɗauka kan waɗanda ake zargi – musamman bayan iƙirarin da ke nuna cewa an ɗaɗe ana cin zarafin yarinyar kuma mahaifiyarta, wadda kurma ce, ta roƙi hukumomi su yi wa ɗiyarta adalci.
Lamarin dai ya fusata mutane da dama har ma zanga-zanga ta ɓarke a wajen ofisoshin ƙaramar hukumar dake Jiangyou.
Fiye da mutum 1,000 ne suka taru kan titi jiya Litinin inda suka kai har tsakaddare a wajen, kamar yadda masu shaguna da ke wurin suka bayyana.
Ɗaya daga cikinsu ya shaida wa BBC cewa “lamarin ya ƙazanta” bayan da ƴansanda suka tarwatsa mutanen da suka taru.
BBC HAUSA