Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a unguwar kotu road cikin birnin Kano ta Kori karar da kamfanin Amart Enterprises ya shigar da Hukumar tace fina-finai bisa neman kotun da ta hana Hukumar tace fina-finai dakatar dasu kan cigaba da kama masu sana’ar tura fina-finai ta downloading a Jahar Kano da sunan kamfanin sun mallaki lasisin copyright.
A zaman da kotun ta yi a lokacin yanke hukunci Mai shari’a Simon A. Amobeda ya ce kotun shi bata da hurumin sauraran karar Hajiya Aisha Amart a saboda haka ya Kori karar wanda hakan tamkar alkalin ya samawa da masu sana’ar tura fina-finan a Jahar Kano rigar kaya ne.
Tsawon lokuta tun a baya kamfanin Amart Enterprises ya shiga takun saka da Hukumar tace fina-finai biyo bayan karar da masu sana’ar tura fina-finai ta downloading na Jahar Kano suka rubutawa Hukumar kan irin gallazawar da suke zargin Hajiya Aisha Amart nayi musu da sunan copyright inda ake kamasu tare da dora musu tara mai tsanani da sunan hukunci saide bayan karbar korafe korafen matasan Shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya nemi kamfanin domin kawo gyara inda dukkannin bangarorin biyu suka yadda tsarin da akazo da shi domin tsaftace kurakuren da ake samu saide daga baya Aisha Amart ta karya tsarin inda hakan yasa Hukumar tasa kafar wando daya da ita dalilin dayasa ta garzaya gaban kotu.
Bayan yanke wannan hukunci Abba El-mustapha ya godewa Allah tare da Kara tabbatar da aniyarsa na tabbatar da yin adalci ga kowa da kowa batare da nuna banbanci ba ko wata alaka ta aiki a masana’antar kannywood.
A karshe ya yi kira da abokanan huldar Hukumar tare da ‘yan masana’antar kannywood dasu cigaba da bashi hadin Kai domin cimma nasarar da aka saka a gaba.