Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti ta bukaci tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose, da ya fice daga jam’iyyar bayan sukar da ya yi mata.
Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na PDP a jihar, Dare Adeleke, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce Fayose ya ci amanar jam’iyya kuma yana ci gaba da bata sunanta duk da cewa yana ikirarin zama cikakken mamba.
Read also: Kano Emirate Tussel:Federal State Courts grant Conflicting Orders
Fayose, a wata hira da aka yi da shi a talabijin, ya ce PDP ta lalace, ruhi da tunaninta sun tafi, yana mai cewa jam’iyyar za ta zo ta hudu a zaben 2027. Ya zargi shugabannin jam’iyyar da raina gudunmawarsa duk da sadaukarwar da ya yi.
Read also: Hukumar Tace Fina Finai Ta Kano Ta Magantu Akan Mawaki Rarara
Sai dai Adeleke ya mayar da martani, yana tambayar dalilin da ya sa Fayose ke ci gaba da zama a jam’iyyar da ya kira “gawa” da “jam’iyyar da ta mutu”.
Ya ce dukkan shugabannin PDP na kananan hukumomi a jihar sun nesanta kansu da Fayose tare da sukar halayensa. Adeleke ya bayyana cewa Fayose bai da tasiri a siyasa kamar yadda yake ikirari, inda ya jaddada cewa PDP za ta ci zaben gwamna a 2026 da ‘yan jam’iyya na gaskiya.
Read also: Gwamnan Kano ya Bada Umarnin Farfaɗo da Makarantar Faransanci da Sinanci
Adeleke ya kammala da cewa PDP a Ekiti tana da karfi kuma ba za ta bar wadanda ke bata mata suna su hana ta ci gaba ba.
Daily Nigerian Hausa

