Khalifa Aminu, fasihin yaron nan mai ƙere-ƙere, ya ƙirƙiri wata sabuwar na’ura mai nuna yanayin jini da jikin ɗan adam.
Ga bayanin na’urar nan da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
“ Wannan shine sabon ‘project’ dina mai ban mamaki da ban al ajabi wato ‘Scan blood🩸& temperature🌡️device’.
“Wato na’urar mai gano bugun jini da yanayin jiki. Wannan na’urar za ta iya temaka wa mutane da dama wajan kare lafiyar jikinsu.
“Ita dai wannan na’urar ana saka ta a hannu ne. Bayan ka saka ta a hannu to duk inda ka shiga idan zafi yai yawa a wajen ko sanyi ko yanayin iskar da ka ke shaƙa to za tayi scaning din jikin ka ta ga yanayin ‘temperature’ din da jikin ka ya ke bukata idan wannan yanayin iskar ko zafi ko sanyi su kai yawa nan take za ta sanar da kai kabar wajen idan ba haka ba zaka iya cutuwa.
“Sannan za ka iya scan din jinin jikin ka don ka ga lafiyar ka kalau ko ba ka da lafiya.
“ Wannan ba karamar fasaha ba ce wajen kula da lafiyar mu…..”
“by khalifa Aminu
Kuyi share din sa da post don bunkasa abun.”
Biz Point