Majalisar dokokin Najeriya ta bayyana damuwa game da babban rashin daidaito tsakanin kudaden da akan kashe wajen ayyukan raya kasa da wadanda akan kashe don gudanar da ayyukan ma’aikatu na yau da kullum a kasafin kudin bara.
Gwamnan Jihar Rivers Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2025
‘Yan majalisar sun yi nuni da yadda aka yi kwauron sakin kudi don aiwatar da manyan ayyukan raya kasa ga ma’aikatu da sassa da hukumomin gwamnati.
‘Yan majalisar dokokin sun ce abin da aka samu bai taka kara ya karya ba, kuma ba zai kai a ce an gudanar da ayyukan yadda ya dace ba a kasafin kudin na bara.
Za a Mayar Da Filin Wasa Na D/K Sansanin Kano Pillars-Kwamishina
Daya daga cikin ‘yan majalisar Injiniya Satomi Ahmed, ya shaida wa BBC cewa an yi shirin aiwatar da karashen kasafin kudin na bara har zuwa watan Yunin bana, ta yadda za a rika aiwatar da shi tare da na wannan shekara.
Kano House Of Assembly Passes 2025 Budget
Yace : “Babbar damuwar ita ce rashin fitar da kudaden da ya kamata a yi manyan ayyuka na ci gaban kasa, rashin hakan shi ne ya haifar da halin da Najeriya ke ciki, da rashin ci gaban gwamnati da matsalolin da ta ke fuskanta.
Ba a bai wa ma’aikatu daban-daban kudaden aiwatar da ayyuka na musamman, kamar fannin noma da tattalin arziki, da ma’aikatar raya yankin Arewa maso yammacin Najeriya ba.
KANET Advocates Budget Tracking Implementation Among CSOs
Wasu ma’aikatun sun samu kashi 40, wasu kuma kashi 30 cikin 100, kai akwai wasu ma da ba su samu kashi 20 ba a kasafin kudin shekarar 2024,” in ji Satomi.
Ya kara da cewa fannin tsaro kamar hukumar leken asiri ta DSS, ma an samu wannan tsaikon, kuma hakan ya janyo musu koma baya na aiwar da ayyukansu.
Katsina State Governor Reshuffles Cabinet to Boost Performance
Wannan ne dalilin da ya sa majalisar dokokin Najeriya, ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya san halin da ake ciki, da kuma bada damar ci gaba da ayyukan a cikin shekarar nan ta 2025, duk da ita ma shekarar na da na ta kasafin kudin, kuma ya amince da hakan.
Shin ko yaya za a gudanar da ayyukan da ba a kammala a kasafin kudin 2024 ba, alhalin kasafin kudin 2025 na nan?
Sai Satomi ya ce: “Babu abin da zai sauya, tun da daman ai ayyuka ne da ba a kammala ba don haka ci gaba da su za a yi, ana kuma yin sababbin ayyukan da za a yi na kasafin kudin bana. Kuma shugaban kasa ya amince da kara wa’adin ci gaba da ayyukan.”
Satomi ya ce za a ga sauyi a kasafin kudin bana, ta hanyar inganta yawan man fetur da ake fitarwa da samun kudaden haraji da hanyoyin samun kudi ta fannin hukumar shige da fice ta Najeriya.
Za kuma su tabbatar an yi amfani da kowanne kudi da aka ware na yin ayyuka a kasafin kudin bana, ba tare da sun bada damar da mutane za su ce sun zama ‘yan amshin shata ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu lura da al’amura a Najeriya ke nuna damuwa kan dimbin bashin da gwamnati ke ci a ciki da wajen kasar, da kuma take fakewa da cewa za a gudanar da ayyukan cigaban ‘yan kasa ne.
BBC HAUSA