Yayin da fargabar samun ɓarkewar annobar murar tsuntsaye a Kano ke ci gaba, gwamnatin jihar ta buƙaci al’umma da su kwantar da hankalinsu tare da kai rahoton duk wani zargi da ake da shi game da cutar ga hukumomin da abin ya shafa.
No Cause for Alarm: Kano Government Addresses Bird Flu Rumors
Raɗe-raɗin ɓullar annobar ya bayyana ne sakamakon wani rahoton da aka samu a watan Disamba na 2024 cewa wani matashi ɗan ƙaramar hukumar Gwale ya sayo agwagwa a kasuwar Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa ya haɗa ta da kajin da yake kiwo.
Nigeria’s Livestock Industry Attracts International Attention-Jega
Daga baya sai ya lura kajin sun fara nuna alamun matsalar numfashi da har ta kai 35 cikin 50 sun mutu. Hakan ya sa ya kai wasu daga cikin waɗanda suka mutu asibitin dabbobi na Gwale domin yin bincike, inda a makon farko na watan Janairun 2025 sakamakon binciken ya nuna murar tsuntsaye ce ta yi sanadin mutuwar tasu.
Samun sakamakon binciken ke da wuya, sai ma’aikatar noma ta je ta kulle wurin da mutumin ke yin kiwon tare da kashe ragowar kajin da yi wa wurin baki ɗaya feshin magani. Haka kuma, ma’aikatar ta yi irin wannan feshin a wurin da ake sayar da kaji a kasuwar Janguza tare da wayar wa masu sanaar kai game da illar murar tsuntsaye.
Kano Revitalizes Job Creation through Livestock Training Institutes
Da tsokaci game da haka, a yau, Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, a cikin wata sanarwar manema labarai daga sashin hulɗa da jama’a na ma’aikatar, ya buƙaci jama’ar jihar nan da su kwantar da hankalinsu saboda lamarin bai kai a kira shi ɓarkewar annoba ba.
Kwamishinan ya ce ma’aikatar lafiya na tsaye sosai a kan al’amarin, tana da ɗaukar dukkan matakan da suka dace na tunkarar matsalar domin daƙile tasirinta kafin ta zama barazana.
L-PRES Organizes Workshop On Improving Livestock Production
Dakta Labaran ya ce kasancewar cutar murar tsuntsaye na harbar mutum tare da haddasa illa ga jiki ya sanya ya kira taro da kwamitocin Kar-ta-Kwana da na Lafiya Guda Ɗaya (Emergency Preparedness Response da One Health) da ke da wakilcin ma’aikatun noma, muhalli da albarkatun ruwa da kuma ƙungiyoyin ci-gaba domin a tattauna tare da tsara hanyoyin da za a tunkari al’amarin.
Ya ce, “Wannan shi muke yi a halin yanzu. Za a rinƙa yin taro da masu ruwa da tsaki a kowane mako. Za a rinƙa sanar da al’umma a kai a kai halin da ake ci game da cutar.
Nigeria’s Livestock Industry Attracts International Attention-Jega
“Za a ƙarfafa sa ido a kowace ƙaramar hukuma, musamman tsakanin masu kiwon kaji da sauran tsuntsaye, sannan za a rinƙa bai wa waɗannan kwamitoci rahoto a kowace rana tare da sanar da Gwamna Abba Kabir Yusuf halin da ake ciki.”
Kwamishinan ya ce alamomin cutar sun haɗa da zazzaɓi, fitar da majina, jan-ido da sauransu, inda ya buƙaci al’umma musamman masu kiwon kaji da su zama jami’an sa ido na farko saboda su kare ababen da suke kiwo da dukiyoyinsu, tare da kai rahoton duk wani yanayi da ke hana kajin walwala ga hukumomin da suka dace domin ɗaukar mataki a kan lokaci.