Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Mai martaba Alhaji Balarabe Tatari, ya aike da sakon ta’aziyya dangane da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Muhammadu Buhari (rtd), da fitaccen attajirin kasuwanci, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, tare da Malam YanKaba da Liman Malam Mansur.
Ambasada Tatari, wanda kuma shi ne shugaban Zauren Kantin Kwari da kuma shugaban Gidajen Kasuwar Kantin Kwari, ya bayyana cewa rasuwar wadannan fitattun mutane babban gibi ne ba kawai ga jihar Kano ba, har ma da arewacin Najeriya da ma nahiyar Afirka gaba ɗaya.
Labari Cikin Hotuna:Aisha Buhari ta Koma KD Domin yin Takaba
A cewarsa, Janar Buhari mutum ne mai jajircewa da rikon gaskiya, wanda duniya ta aminta da amincinsa da kyawawan halayensa.
“Al’umma da dama sun shaida kyawawan ayyukansa da kishin ƙasa,” in ji shi.
Game da Alhaji Aminu Dantata, Ambasada Tatari ya ce duniya ba za ta taba mantawa da gudummawar da ya bayar ba wajen jinƙai da walwalar al’umma. Ya ce:
“Na kai masa ziyara bayan na zama sarki, na sanar da shi matsalolin ‘yan kasuwa, ya umarce mu da mu nemi fili daga gwamnati domin ya gina mana kasuwa kyauta. Mun yi iya kokarinmu, har mun sanar da jama’a ta rediyo, amma Allah bai nufa ba.”
Ya bayyana cewa Alhaji Dantata mutum ne mai arziki da niyyar ci gaban al’umma, kuma akwai abubuwan da suka rage su ne gwanin damuwa.
“Allah ya jikan shi, ya karɓi rayuwarsa cikin rahma, ya azurta shi da Aljanna Firdausi,” in ji shi.
Tinubu, African Leaders Pay Last Respects as Buhari Is Buried
Ambasadan ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, musamman dangin Alhaji Aminu Dantata, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Malam YanKaba da Liman Malam Mansur, tare da al’ummar jihar Kano da gwamnatin jihar baki ɗaya.
Ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan, ya jikan su da rahma, ya sanya su cikin gidan Aljanna Firdausi.