Masarautar hausawan duniya wadda aka fi sani da Al’ummar hausawan duniya organization a turance ta nada shugaban kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari Alhaji Balarabe Tatari a matsayin jakadan zaman lafiya na Africa wato peace ambassador.
An gudanar da taron ne a ranar bikin hausa ta duniya a rufaffen dakin taro na Sani Abacha dake Kofar Mata a Kano.
Da yake jawabi Jim kadan bayan nadin na shi a matsayin jakadan zaman lafiya Alhaji Balarabe Tatari yayi godiya ga Allah subhanahu wata’ala daya nuna mishi wannan rana.
Ta Kuma bayar da tabbacin cewar zai cigaba da jajircewa wajen ganin cewa ya inganta harkokin zaman lafiya.
Balarabe Tatari yayi kira ga alumma da su kaunace juna tare da gujewa duk wani abu da zai haifar da rabuwar kawuna Wanda hakan babban gibi ne ga cigaban Kasar Nageria.
Shugaban kasuwar ta Kantin Kwari ya ce a matsayin su na shuwagabannin ‘yan Kasuwar Kofar su a bude ta ke wajen karbar shawarwari da yin duk Mai yiwuwa wajen ganin Sun sauke nauyin daya rataya a wuyan su.
Ambasada Balarabe ya ce an kirkiri ranar hausa ta duniya ne domin sanin asalin hausawa nagartattun halayen su adabi hikima da sarrafa harshen.
“Tare da gudanar da bajekilin abubuwan da suka danganci al’ada da Kuma wasannin gargajiya”
Ya ce hausawa na bayar da muhimmiyar gudummawa wajen inganta al’adu a fadin duniya baki daya.
Shugaban ya Kuma yi godiya ga kwamishiniyar harkokin al’adu wadda ta wakilci gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Sauran Sun hada da shuwagabannin hadaddiyar kungiyar ‘yan Kasuwar Kantin Kwari da shuwagabannin gidajen Kantin Kwari da sarkin Kasuwar Kantin Kwari da Alhaji Yahaya Bala da dan takarar shugabancin karamar hukumar Gwale Alhaji Ali Isah Musa.
“Da dukannin masoya na da yan’uwa da abokan arziki da suka samu damar halartar bikin nadin”