Gwamnatin Jihar Kano ta fara biyan fiye da Naira biliyan 16 na hakkokin da suka dade suna jiran biya ga tsofaffin kansiloli da sabbin ma’aikatan siyasa a kananan hukumomi 44 na jihar.
A wani biki da aka gudanar a Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an yanke hukuncin biyan ne saboda adalcinsa da mutunta ayyukan da suka yi, tare da jaddada cewa kowane mai wa jihar hidima ya cancanci yabo da biyan hakkinsa ba tare da la’akari da jam’iyyar da ya fito ba.
Rarraba Biyan Kudin:
Sashe na A (2014–2017):
Naira biliyan 1.8 ga mutane 903
Sashe na B (2018–2020):
Naira biliyan 5.6 ga mutane 1,198 (za a biya daga Mayu zuwa Yuli 2025)
Sashe na C (2021–2024):
Naira biliyan 8.2 ga mutane 1,371 (za a biya daga Agusta zuwa Nuwamba 2025)
Kari na Naira biliyan 1.27:
Don kudin haya da kayan daki na ma’aikatan siyasa na yanzu a matakin kananan hukumomi
Gwamnan ya ce wadanda za su ci gajiyar biyan sun hada da kansiloli, shugabannin kananan hukumomi, mataimakansu, mashawarta, da sauran shugabannin da suka gama wa’adinsu ba tare da an biya su hakkokinsu ba.
Ya bayyana cewa wannan biyan ba kyauta ba ne, hakki ne da gwamnatin sa ke dauka da muhimmanci.
Ya kuma yaba da kokarin kwamitocin tantancewa da ma’aikatan kudi da suka taimaka wajen tabbatar da wannan nasara.
“Mu hadu guri guda wajen gina Kano mai inganci da ci gaba,” in ji Gwamna Yusuf yayin kaddamar da mataki na farko na biyan kudaden.