Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano yayi kira da kada a shiga zanga-zangar tsadar rayuwa irin wadda aka shiga a baya kamar yadda ake raɗe-raɗi.

Kwamitin zaman lafiya na jihar Kano ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a nan jihar Kano, ƙarƙashin Jagorancin shugaban skatariyar Amb. Ibrahim Waiya.

Kwamitin zaman lafiyar yaja hankalin masu shirya wannan zanga-zangar kamar yadda ake raɗe-raɗi inda yace “babu wani Ɗa mai ido da zanga-zangar da aka gudanar a baya ta haifar face asarar dukiyoyi ta gwamnati dama wanda basu ji – basu gani ba, musamman idan aka duba abinda ya faru a jihar Kano yadda wasu da ake zargi marasa kishin ƙasa sunyi amfani da wannan damar wajen tura yara wanda basa kishin jihar suka afkawa kayan gwamnati dama ƴan kasuwa”.

Amb. Waiya yace akwai hanyoyin kiranye ga shugabannin da al’umma suke ganin sun gaza wajen kare muradun su da kawo musu canji wanda kudin tsarin mulkin ƙasa ya tanada ya kuma baiwa masu zaɓe damar aikata hakan a duk sanda suke ganin Yakamata.

A ƙarshe Waiya ya tabbatarwa al’umma musamman na jihar cewa babu Kano a shiga wannan zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu ke yunkurin shiryawa.

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version