Shahararren ɗan siyasa kuma tsohon ɗan takara mataimakin gwamnan jahar Kano a jam’iyyar APC Alhaji Murtala ya sule Garo ya taya daukacin al’ummar Musulmi murna bikin sallah karama.
Hakazalika, Alhaji Murtala ya kara da cewa , A dai-dai lokacin da muke gudanar da bukuwan karamar sallah kamar yadda aka saba, kada mu manta da muhimman darusan da muka koya cikin watan Ramadan wadanda suka hada da hakuri da yafiya da jin kai da kuma taimakon juna.
Kano Attorney General Felicitates Governor, Residents on Eid Al Fitr
Azumin watan Ramadan kamar yadda malamai su kai ta fadarkarwa wani kebantaccen lokaci ne da kan karato da bawa zuwa ga ubangijinsa, inji Garo.
Sannan , Manufar darusan da ke cikin wannan wata mai alfarma shi ne , ci gaba da wanzuwa cikin al’umma don samun al’umma ta Gari.
Ina kira ga al’ummar Musulmi musamman na wannan jihar Kano da su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da yalwar arziki mai dorewa.
K-SAFE Co-Chair Sends Heartfelt Eid Wishes
Alhaji Murtala Sule Garo yayi wa kuma yi wa kowa fatan alkairi tare da addu’ar Allah ya karbi ibadinmu ya kuma bamu lafiya da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki. Amin.