Gwamnonin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP sun soke dakatarwar da aka yi wa muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Iliya Damagum.

Gwamnonin sun kuma soke dakatarwar da aka yi wa sakataren hulɗa na ƙasa na jam’iyyar, Debo Ologunagba, da mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Kamaldeen Ajibade.

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da shugaban gwamnonin jam’iyyar kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi wa manema labarai a safiyar yau Talata.

Bala ya ce Damagum ne shugaban jam’iyyar da suka sani yanzu kuma shi zai ci gaba da riƙe kujerar.

Tun da farko dai, wani ɓangaren kwamitin zartaswar jam’iyyar na ƙasa da ya ɓalle ya sanar da naɗa Yayari Mohammed a matsayin wanda zai maye gurbin Damagum, inda kowane ɓangare ya yi iƙirarin dakatar da ɗayan.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Yayari ya ce kwamitin zartaswar jam’iyyar ya naɗa shi ne domin mayar da dawo da jam’iyyar kan turba.

Ya ce PDP ba ta yin adawa yadda ya kamata saboda kowa ya ɗora buƙatar kansa a gaba kafin ta jam’iyya – musamman ma wasu jagororin kwamitin na zartaswa.

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version