Sabuwar Daraktar Harkokin Ma’aikata (DPM) ta Karamar Hukumar Gwarzo, Hajiya Zulai Sabo Usman, ta kama aiki a hukumance, inda ta yi alkawarin yin aiki tare da ma’aikata domin ci gaban yankin.
A wajen taron, Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, ya tabbatar da cewa za su yi aiki tare cikin jituwa.
Ya kuma bukaci ma’aikata da su ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai kamar yadda suka yi wa wanda ya gabata.
Alummar Gwarzo Sun Yi Fitar Dango Don Tarbar Sabon Hakimin Su
Dr. Mani ya yi fatan alheri ga tsohon DPM na yankin, Alhaji Ubale Magaji, wanda aka tura zuwa Karamar Hukumar Ungogo domin ci gaba da aikinsa.
“Ina kira ga ma’aikatan karamar hukuma da su hada kai da sabuwar DPM domin samun ci gaba mai sauri a Gwarzo,” in ji shi.
A nata jawabin, Hajiya Zulai Sabo Usman, wadda ita ce Mataimakiyar Shugabar Kungiyar DPMs na kananan hukumomi 44 a jihar, ta gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa da kuma Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarautu bisa goyon bayansu.
Ta tabbatar da cewa za ta yi aiki tare da ma’aikata domin ganin an samu cigaba mai dorewa a yankin.
KH Gwarzo Ta Kafa Kwamitin Rijiyoyin Burtsatsai Da na Kudin Shiga
A nashi jawabin, tsohon DPM, Alhaji Ubale Magaji, ya gode wa shugaban karamar hukuma da ma’aikatan yankin bisa hadin kai da suka bashi a lokacin da yake kan kujerar.
Shi ma da ya yi jawabi, Alhaji Musa Maitama, DPM na Karamar Hukumar Minjibir kuma Shugaban Kungiyar DPMs na kananan hukumomi 44, ya bayyana Hajiya Zulai Sabo Usman a matsayin shugaba mai nagarta da kwazo, wadda za ta inganta cigaban Gwarzo.
Taron ya samu halartar Sakataren Karamar Hukuma, Alhaji Sunusi Abdullahi Getso, CPO na yankin, Alhaji Umar A. Rano, da Shugaban NULGE reshen Gwarzo, Comrade Sani Muhammad Gwarzo.
Haka zalika, an samu halartar kansiloli zababbu da na nada, masu ba shugaban karamar hukuma shawara, ma’aikata daga Karamar Hukumar Bebeji da sauran ‘yan siyasa daga yankin.