Majalisar Masarautar Kano ta fitar da wata takarda mai dauke da umarni ga dukkan Hakimai da ‘Yan Majalisa na masarautar da su hallara a Birnin Kano domin halartar bikin hawan Babbar Sallah da za a gudanar cikin makon gobe.
A wata takardar sanarwa da Sakataren Majalisar Masarautar Kano, Alhaji Abba Yusuf Danmakwayon Kano ya rattabawa hannu, an bukaci Hakimai da sauran shugabannin gargajiya da su iso Kano tare da dawakan su da mahayan su a ranar Laraba, 8 ga Dhul Hijjah, 1446 Hijira, wanda ya yi daidai da 4 ga Yuni, 2025.
Bayan haka, ana sa ran za su halarci Fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Alhamis, 9 ga Dhul Hijjah, wato 5 ga Yuni, 2025 da misalin karfe 11:00 na safe, domin karbar umarni da bayani kai tsaye daga Sarkin Kano.
Daga nan kuma za a gudanar da wani taro da Hakimai a dakin taron Majalisar Masarauta dake Kofar Kudu, inda za a fayyace tsarin gudanar da hawan Babbar Sallah na bana.
Majalisar ta kuma tabbatar da cewa an tuntubi shugabannin kananan hukumomi domin saukaka shigowar Hakiman daga yankunansu zuwa Birnin Kano.
A karshe, majalisar ta roki Allah da ya sanya a gudanar da bikin Babbar Sallah cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.