Shugaban Kwamitin Kula da Bincikicen kadarori da aka kafa a Karamar Hukumar Ungogo, Dr. Saminu Umar Rijiyar Zaki, ya kammala aikinsa yakuma gabatar da rahoton shugaban riko na karamar hukumar ungogo Alh sani Abdu ungogo a ofishin sa.

Rahoton, wanda ya ƙunshi ayyukan cigaba, da ƙalubalen da karamar hukumar ta fuskanta yayin lokacin sauyin shugabanci.

Dr. Saminu Umar ya nuna godiya bisa damar da aka ba shi na jagoranci tare da jaddada manyan bangarori da za a mayar da hankali kansu a lokacin shugabancin sa, wandanda suka hada da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da haɗin kan al’umma.

READ ALSO: Kano Enhances Healthcare Service Delivery With Revised DRF

Jami’in rikon na karamar hukumar ungogo Alh sani Abdu bayan karɓar rahoton, ya yabawa Dr. Saminu Umar da dukkan kwamitin kula da canji bisa ƙwazo da jajircewarsu.

SIMILAR: Da Dumi-Dumi: Shugaban karamar hukumar Ungogo Engr Abdullahi Ramat ya yi murabus

Ya tabbatar da cewa za a binciki aiyyukan kwamitin da yakawo tare da shawarwari da suka bayar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version