Gwamnatin Najeriya, FG, ta ce daga mako mai zuwa ne za a fara aiwatar da umarnin da ta bayar na dakatar da karbar haraji a kan kayayyakin abinci da ake shigar da su kasar daga waje.
Tun a watan Yuli ne gwamnatin ta sanar da cewa ta amince da wa’adin kwana 150 na shigar da masara da shinkafa da alkama daga waje ba tare da biyan haraji ba, domin magance matsalar tsadar kayan abinci a kasar, to amma har yanzu ba a ga hakan ba, inda ‘yan kasuwa ke korafi da cewa ba su gani a kasa ba.
To amma da yake jawabi a lokacin taron shugabannin hukumomin tsaro na kasar da aka yi jiya Talata a Abuja, shugaban hukumar hana fasa kwauri, Bashir Adeniyi, ya ce za a fara aiwatar da shirin da zarar an kammala tsara ka’idojin da aka shimfida.
Ya ce: “Ana fayyace ka’idojin a ma’aikatar kudi, kuma ina tabbatar muku cewa zuwa mako mai zuwa, za a kammala fitar da ka’idojin…’’
Ya ce an samu jinkirin aiwatar da tsarin ne domin ganin an yi laka’ari da yadda zai amfani dukkanin masu ruwa da tsaki da suka hada da manoma.
Shugaban na kwastan ya ce tuni ma wasu daga cikin kayan abin sun riga sun shigo kasar, kuma za a fitar da su ba tare da biyan haraji ko kudin fito ba.
BBC Hausa