Gwamnatin jihar Kano tace zata mayar da karamin filin wasa na Dawakin kudu sansanin da za ta dinga killace ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano pillars a duk lokacin da zasu fafata wasa a gida.

Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala kare kasafin kudin ma’aikatar sa na shekara mai kamawa.

Kwankwaso yace daga cikin ayyukan da gwamnati ta sahalewa ma’aikatar sa gabatarwa a cikin kasafin kudin na shekara mai kamawa har da gyaran dukkanin filayen wasanni mallakin gwamnatin Kano wadanda suka hadar da kammala gyaran filin wasa na Sani Abacha.

Da na Sabon Gari da takwaran su na Gwagwarwa da Kuma mayar da filin wasa na Dawakin kudu sansanin ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar ta Kano pillars.

Kwamishinan ya Kara da cewa a cikin kasafin na shekara mai kamawa dai ma’aikatar sa zata mayar da hankali Kan koyawa matasa sana’o’I da basu Jari domin dogara da kai.

Kwamishia Mustapha Kwankwaso ya sha alwashin habaka harkokin matasa ta kowane fanni la’akari da yadda matasan suke da mafi rinjayen adadi a cikin al’ummar jihar Kano

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version