
A wani muhimmin mataki na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da rabon gidan sauro Mai sinadarin kashe sauro har guda 189,600 ga al’umma a fadin yankin.
An kaddamar da wannan aikin ne a asibitin ’Yar Kasuwa da ke unguwar Alkalawa a cikin garin Gwarzo, inda jami’an lafiya suka bukaci al’umma da su rika amfani da gado-gadon a kullum domin kariya daga cutar.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban hukumar samar da Lafiya a matakin Farko na Karamar Hukumar, Alhaji Sulaiman Abdulqadir Karaye, wanda ya wakilci Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, ya bukaci musamman mata da su kula da yadda ake amfani da gado-gadon.
NAFDAC Warns of Falsified Malaria Medication in Circulation
“Ina shawartar jama’a kada su wanke ko su sayar da gado-gadon nan. A rika amfani da su kowace dare domin samun cikakkiyar kariya daga cizon sauro da cutar zazzabin sauro,” in ji shi.
Alhaji Sulaiman ya kuma yaba wa Shugaban Karamar Hukumar, Sarkin Gwarzo, Gwamnatin Jihar Kano, shugabannin gargajiya, ma’aikatan lafiya da daukacin al’umma bisa hadin kan su wajen yaki da cututtuka.
A yayin taron, an mika takardar yabo ga Sarkin Gwarzo, Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano, Alhaji Bello Abubakar Gwarzo, saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen goyon bayan shirye-shiryen lafiya a yankin. An wakilce shi a wajen taron da Malam Kabiru Muhammad.
Shi ma da yake jawabi, jami’in wayar da kan jama’a kan harkokin lafiya, Alhaji Abubakar Musa Karaye, ya shawarci al’umma da su rataye gado-gadon a waje mai inuwa na tsawon sa’o’i kafin fara amfani da su, saboda karfin maganin da aka saka a ciki.
A nasa bangaren, Sarkin Gwarzo, ta bakin wakilinsa, ya yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, saboda kokarin da suke yi wajen bunkasa harkar lafiya da yaki da zazzabin cizon sauro.
UNICEF Urges Kano to Extend Maternity Leave, Invest More in MNCH
Ya bukaci al’umma da su mayar da amfani da gado-gadon sauro na kowace dare tamkar wani bangare na rayuwar su domin kauce wa kamuwa da cututtukan da sauro ke yadawa.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da kayan, ciki har da Malama Bilkisu Usman da Saifu Muhammad, sun nuna jin dadinsu tare da gode wa Gwamnatin Kano, Shugaban Karamar Hukumar da hadin gwiwar kungiyoyin ci gaba bisa wannan kyauta mai muhimmanci da zata kare rayukan jama’a.
Wannan gagarumin shiri na daga cikin matakan da Gwamnatin Jihar Kano da kananan hukumomi ke dauka domin rage yawan kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kare lafiyar jama’a, musamman yara da mata masu juna biyu.