Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da ingancin aikin jarida tare da kiyaye ka’idojin aiki, da kuma ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tsaftace fagen yada labarai.
Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a lokacin da kungiyar Young Female Professionals in Media (YFPM) ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.
Gwamnatin Jihar Kano Bata Hana Yin Adawa Ba- ComradeWaiya
Comrade Waiya ya bayyana cewa, koyaushe ma’aikatar ta na ganin muhimmancin yin aiki kafada da kafada da kungiyoyi wajen ci gaba da bunkasa harkokin yada labarai a jihar.
Ya yabawa kungiyar YFPM bisa jajircewarsu wajen kare darajar aikin jarida, yana mai cewa wannan yunƙuri ya zo a kan gaba da kuma daidai da manufar ma’aikatar wajen inganta aikin jarida mai ma’ana.
“A yau aikin jarida ya fuskanci kalubale na rashin bin ka’idoji, ba kawai a dandalin sada zumunta ba har ma a jaridun gargajiya. Wannan babban abin damuwa ne gare mu a matsayin gwamnati, saboda yana bata sunan jiharmu da kuma aikin jarida gaba ɗaya. Wannan ne ya sa muka kuduri aniyar yin aiki tare da kungiyoyi irin naku don dawo da mutunci da kima a aikin jarida,” in ji Waiya.
Na Farfado da Martabar Gidan Rediyon Kano- Kwamared Rano
Ya ƙara da cewa, Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Ƙwararrun ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ) sun amince da kafa kwamiti na dattawan ’yan jarida da za a kira da League of Veteran Journalists, domin tsara dabarun da za su ƙarfafa bin ka’ida da nagarta a aikin jarida.
Kwamishinan ya tabbatarwa kungiyar YFPM da cikakken goyon bayan ma’aikatar ga duk wani yunƙuri da zai taimaka wajen tsaftace harkar yada labarai da inganta ƙwarewar ’yan jarida.
A nata jawabin, Sakatariyar YFPM, Maryam Usman Nagado, ta bayyana cewa kungiyar ce ta farko a tarihin Kano da ta haɗa ƙwararrun matan ’yan jarida a wuri guda
Ta ce sun zo ma’aikatar ne domin gabatar da kansu da kuma neman haɗin gwiwa ta hanyar kulla yarjejeniya (MoU) a fannoni da suka haɗa da horaswa, wayar da kan jama’a, ilimin jarida, da kuma ƙarfafa mata a aikin jarida.
Nagado ta ƙara da cewa YFPM ta ƙunshi matan ’yan jarida, masu gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai, waɗanda ke da kishin koyar da sababbin ’yan jarida, ƙarfafa bin ka’ida, da kuma taimakawa ci gaban al’umma ta hanyar jarida mai ɗorewa.
Kungiyar ta yaba wa kwamishinan bisa irin ƙoƙarin da yake yi don kawo sauyi mai ma’ana a harkar yada labarai a jihar Kano.