Wata mata ƴar Amurka wadda ta ɗauki ciki tare da haife jariri namiji ba tare da sanin cewa ba ɗanta ba ne ta fara ɗaukar matakin shari’a kan asibitin da ke taimaka wa mata samun ciki ta hanyar dashen ɗantayi (IVF).
Kotu Ta Ki Bayar Da Belin Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Kaduna
Tana zargin asibitin da yi mata dashen ɗantayin da ba nata ba, bayan an tilasta ta ta mayar da mayar wa asalin iyayen jaririn ɗansu.
Krystena Murray, mazauniyar jihar Georgia, ta ɗauki cikin ne bayan dashen ɗantayi (IVF) da aka yi mata a asibitin masu neman haihuwa da ake kira Coastal Fertility Clinic, a watan Mayun 2023.
To amma daga baya an gano cewa ɗantayin da ta rena a cikinta na wasu ma’auratan ne daban.
Hakan ya fito fili ne bayan da Ms Murray ta haifi jaririn da bai yi kama da ita ko wanda ya ba ta gudumawar maniyyi ba.
Kotun Daukaka Kara ta kama Trump da laifin Cin Zarafin Yarjarida
Duk da haka, Ms Murray ta so a bar mata yaron, inda ta ci gaba da renon shi har tsawon watanni, har sai da hukumomi suka bai wa ainahin iyayen ikon karɓe ɗansu.
A cikin wani bayani da ta sanar ta hannun lauyanta, Murray ta ce: “Na ɗauki jaririn nan a cikina, na kamu da son shi, na haife shi, sannan na shaƙu da shi sosai, irin shaƙuwa ta ɗa da uwa, amma yanzu an ƙwace shi. Ba zan taɓa samun sauƙin wannan takaiciba.”
Murray wadda baturiya ce ta haifi jaririn, wanda ya kasance baƙar fata a watan Disamban 2023. Ta ƙi sanya hotunan jaririn a shafukan sada zumunta sannan ta ƙi bari ƴan’uwa ko abokanta su gan shi.
Daga nan ne ta sayi abin gwajin gano halittar gado, wanda za ta iya yin gwajin a gida.
Sakamakon da ta samu a watan Janairun 2024 ya tabbatar mata cewa jaririn ba shi da alaƙa da ita, kamar yadda ta bayyana a koken da ta rubuta game da asibitin.
Bayan wata ɗaya, ta sanar da asibitin game da lamarin. Asibitin ta sanar da asalin iyayen jaririn, waɗanda su kuma suka kai ƙara domin karɓar ɗan nasu, lokacin da yake da wata uku a duniya.
Ala tilas Murray ta miƙa jaririn bayan lauyoyinta sun tabbatar mata cewa ba za ta samu nasara ba idan ta je kotu da nufin a bar mata jinjirin.
A halin yanzu jaririn na hannun iyayensa na asali a wata jiha, inda suka sauya masa suna.
Koken da Murray ta shigar ya bayyana cewa har yanzu ba ta san ko asibitin Coastal Fertility ya bai wa wasu nata ɗantayin ba ne ko kuma a’a.
A wani saƙo da ya tura wa kafar talabijin ta CBS News, asibitin ya amince cewa ya tafka kuskure, sannan ya nemi afuwa game da halin da ya jefa matar a ciki.
“Wannan ne kuskure ɗaya da muka yi, kuma bai shafi wasu mutanen da muka bai wa kulawa ba,” kamar yadda asibitin ya sanar a bayaninsa.
“A ranar da aka gano wannan kuskure mun sake yin nazari mai zurfi kan ayyukanmu tare da ɗaukan matakan kariya domin kare masu zuwa neman magani a wurinmu ta yadda ba za a sake samun irin haka ba.”
A shekarun baya-bayan nan an shigar da ƙararrakin asibitocin maganin haihuwa da dama kan yin kuskure wajen dashen ɗantayi.
IVF wani tsari ne da ake haɗa ƙwan haihuwar mace da maniyyin namiji a kwalba kafin a dasa ɗantayin a cikin mahaifar mace domin reno a matsayin juna-biyu.
BBC HAUSA