Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti ta bukaci tsohon gwamnan jihar, Ayodele Fayose, da ya fice daga jam’iyyar bayan sukar da ya yi mata.
Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na PDP a jihar, Dare Adeleke, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce Fayose ya ci amanar jam’iyya kuma yana ci gaba da bata sunanta duk da cewa yana ikirarin zama cikakken mamba.
Fayose, a wata hira da aka yi da shi a talabijin, ya ce PDP ta lalace, ruhi da tunaninta sun tafi, yana mai cewa jam’iyyar za ta zo ta hudu a zaben 2027. Ya zargi shugabannin jam’iyyar da raina gudunmawarsa duk da sadaukarwar da ya yi.
Sai dai Adeleke ya mayar da martani, yana tambayar dalilin da ya sa Fayose ke ci gaba da zama a jam’iyyar da ya kira “gawa” da “jam’iyyar da ta mutu”.
Ya ce dukkan shugabannin PDP na kananan hukumomi a jihar sun nesanta kansu da Fayose tare da sukar halayensa. Adeleke ya bayyana cewa Fayose bai da tasiri a siyasa kamar yadda yake ikirari, inda ya jaddada cewa PDP za ta ci zaben gwamna a 2026 da ‘yan jam’iyya na gaskiya.
Adeleke ya kammala da cewa PDP a Ekiti tana da karfi kuma ba za ta bar wadanda ke bata mata suna su hana ta ci gaba ba.
Daily Nigerian Hausa